Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraniya ya umarci dukkan majiya ƙarfin ƙasar sa su ɗauki bindiga su kare ƙasar su.
“Ukraniya za ta bai wa kowane matashi maji ƙarfi bindiga matsawar ya na so ya tashi ya kare ƙasar sa.
“Ku yi shirin goyon bayan ƙasar mu Ukraniya a cikin biranen mu.” Inji shugaban.
“Mun yanke hulɗa kowace iri da Rasha. Duk wanda ya san ba shi da wani ɗarsashin ƙaunar Rasha, ya fito ya yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da harin da ta kawo mana.
“Rasha ta kawo mana hari da safe. Kamar irin yadda dakarun Nazi na Jamus su ka kawo mana a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu.
“A yau mun raba hanya. Rasha ta kama turbar shaiɗan. Ukraniya ya kama turbar kare kan ta daga harin shaiɗanu. Kuma ko za a daka mu a ƙulƙula a cikin turmi, ba za mu miƙa ‘yancin mu a hannun Moscow ba.”