Ma’aikatar Harkokin wajen Najeriya ta bayyana cewa harin da kasar Rasha ta kai wa makwabciyar ta kasar Ukraine ya yi matukar bata mamaki.
Ma’aikatar ta ce bisa ga bayanan da ta samu game da abinda ke faruwa a kasar zuwa yanzu shine ƙasar Rasha na kai hari sansanoni sojojin kasar Ukraine ne ba gidajen jama’a ba.
Sai dai kuma bisa ga rahotannin manyan kafafen yaɗa labarai kamar su BBC da CNN, an nuna yadda rokokin Rasha ke sauka a gidajen mutane.
An nuna wasu da dama da rauni a jikkunansu amma kuma Najeriya bata yi tir da hareharen Rasha ga Ukraine ba.
Discussion about this post