A zaman majalisar Jigar Zamfara ranar Laraba, majalisar ta tsige mataimakin gwamnan jihar Mahdi Gusau.
Majalisar ta naɗa Sanata Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar Zamfara.
Mahdi Gusau ya saka kafar wando ɗaya da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle tun bayan ƙin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da yayi.
Majalisar jihar ta tuhume shi da wasu laifuka wanda Mahdi ya fito ya bayyana cewa ba zai bayyana a gabanta ba saboda maganar zargi da ake masa ya na gaban kotu.
Hakan bai hana majalisar tsige shi a a yau Laraba ba.
Kakakin majalisar Nasiru Magarya ya ce kwamitin da majalisar ta naɗa ya tabbatar da laifukan da Mahdi ya aikata wanda a dalilin haka ya sa majalisar ta tsigeshi.
Discussion about this post