A ranar Talata ce aka gabatar da wani ƙudiri a Zauren Majalisar Tarayya, wanda ke neman a rushe Hukumar Tsaro ta NSCDC, wato jami’an ‘Sibul Difens’.
Ɗan Majalisar Tarayya daga Oyo, Shina Peller ne ya gabatar da ƙudirin, inda ya nemi a soke Dokar NSCDC ta 2007, wacce ta halasta kafa hukumar.
Ƙudirin ya nemi cewa idan aka rushe NSCDC, to a maida dukkan kadarorin hukumar da jami’an ta ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.
Kudirin ya nemi a kafa wani kwamiti wanda zai sa-ido da lura wajen tabbatar da an kwashi komai da komai na NSCDC an damƙa ga Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya.
Peller ya ce dukkan ayyukan da NSCDC ke yi, ayyuka ne da dokar ƙasa ta wajibta wa ‘yan sandan Najeriya su yi, kuma su na yi ɗin.
“Ayyukan da NSCDC ke yi duk ayyukan da ‘Yan Sandan Najeriya ke yi ne. Rarraba aikin ‘yan sanda ga NSCDC dafkal ne, kuma asarar maƙudan kuɗaɗe ce. Sannan kuma ana samun saɓanin da bai kamata a ce ya na faruwa ba.”
Ya ce a duk shekara ana yin asarar Naira biliyan 100 haka kawai wajen kasafin kuɗin ayyukan hukumar, wadda dukkan aikin da su ke yi, ‘yan sanda na yin su.
Dokar NSCDC ta 2003 ce ta kafa hukumar a ƙarƙashin mulkin Obasanjo.
“Sashe na 5 (3) ya ba jami’an NSCDC ƙarfin kama wanda ake zargi da laifi, ko da sammaci ko babu sammaci daga kotu. Za su iya kamawa, su tsare, su yi bincike, sannan su gurfanar a kotu, kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar.”
Wannan ƙudiri dai zai tsallake uku kafin a amince da shi har a nemi ya zama doka.