Da talakan Najeriya zai ajiye siyasar ƙabilanci, ɓangaranci da duk wani ‘ci’ ‘cin’ da ke cin zukatan ‘yan Najeriya, to da sai su yi tururuwa su nuna wa Rochas Okorocha cewa su ‘ya’yan halas ne, su maka masa ƙuri’u, idan har APC ta tsayar da shi daga ɓangaren ƙabilar Kudu maso Gabas.
Rochas ɗan ƙabilar Igbo wanda ya shahara wajen amfani da maƙudan kuɗaɗen sa, sama da shekaru 20 kafin ma ya shiga siyasa, wajen amfana wa dubban marasa ƙarfi a ɓangaren ilmantarwa da sauran fannoni daban-daban.
A Arewacin Najeriya akwai miliyoyin attajirai da manyan masu riƙe da mulki, kai har ma da karta-kartan ɓarayin gwamnati, waɗanda al’ummar su ba su amfanar su, amma su na amfana da Rochas Foundation, gidauniyar da kusan ita ce farko da yawan mutanen Arewa suka fara sani da suna ‘Gidauniya’ ta tallafa wa marasa ƙarfi.
Idan aka cire adawa, Najeriya na buƙatar mutane irin su Okorocha, wanda ba shi da ƙabilanci, kuma addinantar da siyasa bai yi tasiri ko ɗarsashi a zuciyar sa ba.
Rochas ya iya Hausa, kuma ya iya zama da Hausawa da sauran ƙabilun Arewa. Haka sauran ƙabilun Kudancin Najeriya.
Ƙalubalen Rochas shi ne ya ƙoƙarta ya samu haɗin kan ‘yan ƙabilar sa ta Igbo. Idan suka nemi kowa ya janye wa Rochas, kuma suka yi masa ruwan ƙuri’u, to tsohon Gwamnan Imo ɗin ba zai yi wahalar nasarar zaɓen 2023 ba.
Daɗa ya rage wa Okorocha ya gina tubalin neman goyon bayan ‘yan Arewa. Su kuma ‘yan Arewa su tuna da irin kulawa da mutuncin da Rochas ya yi masu tsawon shekara da shekaru wajen inganta rayuwar ƙananan yara ta hanyar ɗaukar nauyin ilmantar da su da sauran ayyukan tallafi.
Idan ana maganar mulki, to nagari ake nema. Shi kuwa Rochas an shaidar shi a ƙasar nan, nagari ne, ba ɗan-garari ba ne.
Mutum dai tara yake bai cika goma ba. Okorocha ya ɗan samu cikas a 2019, bayan cikar wa’adin mulkin sa a Jihar Imo, inda ya tsayar da surikin sa takarar gwamna. Ko ma dai mene ne, ba za mu ce sun san sirrin cikin sa ba.
Waccan tarangahuwar neman tsayar da surikin sa dai ta wuce, yanzu 2023 ake magana. Ba a dai san maci-tuwo ba inji Hausawa, sai miya ta ƙare.
Shi kuwa Rochas ya fito neman takarar shugabancin ƙasa. Saboda ƙoƙarin nuna cewa shi na kowa ne, har ayar Alkur’ani ya jawo a wurin ƙaddamar da sanarwar fitowar sa takara. Inda ya ƙara burge mutane, bayan ya ja baƙin kuma sai ya fassara da kan sa.
To, saura dai shekara ɗaya a yi zaɓe. Kuma ko ma dai me kenan, mai hankali kaɗai zai iya gane ɗingishin kwaɗo.
Discussion about this post