Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari inda ya yi masa bayanin halin matsalar tsaro da jihar ke ciki.
Da ya ke bayani ga manema labarai bayan ganawar sa da Buhari a keɓance, Yahaya Bello ya ce masu jihar Kogi an samu zaman lafiya, sanadiyyar tsauraran matakan tsaron da gwamnatin jihar ta ɗauka.
Gwamnan ya ce ‘yan Najeriya baki ɗaya na da rawar da kowa zai taka wajen tabbatar da tsaro a faɗin ƙasar nan.
Daga nan sai ya yi kira ga al’ummar ƙasar nan su tashi tsaye zama wasu ejan-ejan masu kai wa jami’an tsaro wajen tona asirin miyagun mutane, domin a samu sauƙin samar ta ingantaccen tsaro a ƙasar nan.
“Na kawo wa Shugaban Ƙasa ziyara ce kamar yadda na saba, don na sanar da shi irin ci gaban da aka samu wajen samar da tsaro a Jihar Kogi.
“Kamar yadda ku ka sani, a lokacin da na hau mulki, Jihar Kogi ce ta fi sauran jihohin ƙasar nan rashin tsaro.
“Amma a yau da taimakon Allah, Jihar Kogi ce ta fi kowace jiha zaman lafiya a Najeriya.
“Kuma Shugaban Ƙasa ya yi matuƙar murna da farin cikin irin waɗannan bayanai da na yi masa, tare da ci gaban da jihar ta samu a ɓangaren tsaro, tattalin arziki, samar da ayyukan bunƙasa harkokin rayuwa na yau da kullum, zaman lafiya da haɗin kai, duk sun wanzu a Jihar Kogi.
“To waɗannan bayanai dai su ne ainihin abin da mu ka tattauna da Shugaban Ƙasa. Kuma ya ce na isar masa da gaisuwa da fatan alheri ga ɗaukacin al’ummar Jihar Kogi.”
Bello ya ce gwamnatin Buhari ya yi gagarimin aiki sosai a fannin inganta tsaro.
Sai dai kuma ya yi ƙorafin cewa kafafen watsa labarai ba su yayata nasarorin da aka samu a fannin tsaro. Ya ce bba wani abu ba ne siyasa ce.
Batun Takarar Yahaya Bello 2023:
Dangane da yiwuwar ɗan takarar APC a Zaɓen 2023 ya fito daga Arewa ta Tsakiya, Gwamna Bello ya bayyana Arewa ta Tsakiya cewa yankin ne aka fi dannewa fiye da sauran dukkan yankunan Najeriya, tun bayan samun ‘yanci a 1960.
A kan haka ne ya ce a zaɓen 2023, yankin Arewa ta Tsakiya ne ya fi dacewa da cancanta.
Bello ya yi maganar ce an matsayin raddi ga shugabannin Ohanaeze Ndi Igbo, masu cewa Yankin Kudu maso Gabas ne ya fi dacewa ya yi mulkin Najeriya a 2023.
Gwamna Yahaya Bello dai ya fi sauran dukkan masu sha’awar fitowa takara nuna maitar sa ta neman shugabancin ƙasa a fili.
Discussion about this post