Kamar yadda aka sani suga abu ne da ake amfani da shi wajen kara dadin abinci irin su kunun aki, fura, cincin da dai sauran su.
Ana samu siga daga cikin rake sannan yana dauke da sinadarin Carbohydrates wanda ke taimakawa wajen samar da karfi a jiki.
Kungiyar likitocin zuciya dake kasar Amurka AHA sun bayyana cewa yawaita Shan kayan zaki na cutar da lafiyar mutum.
Wadannan cututtuka sun hada da ciwon siga, kiba, rage kaifin kwakwalwa da haddasa yawan mantuwa, dajin dake kama dubura, hawan jini, ciwon huhu, ciwon Koda da dai sauran su.
Likitocin sun ce cin abincin dake dauke da sinadarin cabonhydrates ya fi inganta lafiyar mutum fiye da shan kayan zakin da ake sha domin sinadarin dake cikin su ne ke cutar da lafiyar mutum.
Adadin yawan sigan da ya kamata yara kanana su sha a rana
Kungiyar AHA sun ce bai kamata ana yawaita bai wa yara siga suna sha ba domin yara na iya kamuwa da cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin yawan shan kayan zaki.
Likitocin sun ce kamata ya yi yara su sha siga cikin cokali ƙasa da shida a rana.
Likitocin sun ce ga maza ya kamata ya su sha cikin cokali 9 a rana sannan mata cikin cokali 6 a rana.
Sai dai abin takaici ne yadda mutane da dama basa kiyaye wa wannan sharadi inda a dalilin haka cututtuka suka yadu kuma suke yawan kisan mutane a duniya.
Likitocin sun kuma ce yawan bai wa yara kayan zaki na cutar da hakoran su, saurin sa yaro ya tsufa da kiba.
Domin kiyaye kiwon lafiyar yara kamata yayi a rage yawan basu kayan zaki.
Mutum zai iya rayuwar ba tare da ya Sha kayan zagi ba.
Likitocin sun tabbatar cewa mutum zai iya rayuwarsa cikin koshin lafiya idan ya daina shan kayan zaki.
Shekarun da ya kamata mutum ya rage shan siga
Likitocin sun ce domin samun koshin lafiya kamata ya yi a rika yin taka tsantsan da shan kayan zaki.
Kamata ya yi duk mai shan kayan zaki ya rika motsa jikinsa domin guje wa kamuwa da cututtuka.
Siga na kashe karfin mazakutan namiji
Cututtukan dake kashe karfin kuzari namiji sun hada da hawan jini, ciwon siga, ciwon Koda da dai sauran su.
A dalilin haka likitocin suka yi kira ga maza da su guji yawan shan kayan zaki domin kare kansu daga kamuwa da wadannan cututtuka dake kashe karfin kuzari namiji.