Gwamnan jihar Akwa Ibom Emmanuel Udom ya bayyana cewa kunh’giyoyin Mayu na jihar sun maka shi a kotu saboda ya na gina katafaren Coci a babban birnin jihar.
Udom ya ce dalilin gina wannan coci shine don ya tabbatar wa mutane cewa lakanin da ake yi wa jihar na ‘jiha ce ta Allah’ ya tabbata.
Waɗannan na daga cikin kalaman da gwamnan yayi a lokacin da yake hira da manema labarai wajen bayyana ayyukan da yayi a jihar tun daga darewar sa gwamna zuwa yanzu.
” Ina so ku sani cewa kungiyoyin mayu sun haɗu kaf ɗin su sun makani a kotu saboda ina gina Coci.Wai sun ce su ba mutane bane da suka yarda da addini. Mun yi nasara a kan sa a Kotu amma sun ɗaukaka kara.
Da aka yi masa tambaya ko da gaske Allah ne yayi masa wahayin wanda zai gaje shi kamar yadda ya faɗi, Udom ya ce mai tambaya ba zai gane yadda abin yake ba ne. ” Al’amari na wahayi da ganawa da ubangiji sirri ne. Shi yasa abin yayi muku wani banbaraƙwai, abin sirri ne.
Sai dai kuma maimakon nasarorin da gwamnatin ta bayyana ta samu a tsawon shekarun mulkinta, sai kuma kowa ya karkata ga maganan mayu da suka kai gwamna kotu kamar yadda ya furta.
Discussion about this post