Kotu ta bada umarnin a tsare wani mai goyon bayan tafiyar siyasar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar a kurkuku, saboda zargin sa da aka yi da cin mutuncin Lamiɗo Adamawa, Barkinɗo Aliyu-Musdafa.
Alƙalin Kotun Majistare ta 1 da ke Yola ne ya bada umurnin tsare Yusuf Baba-Yola, lokacin da ‘yan sanda suka gabatar da shi a kotu.
‘Yan sanda sun gurfanar da Baba-Yola a kotu ne bayan da masarautar Adamawa ta kai koken sa a ofishin su.
Lamarin ya faru ne dai lokacin da saɓani ya shiga tsakanin Baba-Yola da wani ɗan siyasa mai suna Baƙo DDK, wanda ya shiga gidan radiyo ya yi kaca-kaca da Atiku, ya na cewa bai tsinana wa mutanen jihar Adamawa komai ba a lokacin da ya ke Mataimakin Shugaban Ƙasa.
DDK wanda mai goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari ne, ya shiga wani gidan radiyo mai suna NAS F.M, ya riƙa lissafa gagarimin ayyukan da gwamnatin Buhari ta yi a Jihar Adamawa. Bayan nan kuma sai ya ƙalubanci magoya bayan Atiku su je su faɗi ayyuka uku da Atiku ya yi a Adamawa.
Ya kuma bayyana irin mutanen jihar Adamawa da Buhari ya naɗa a muƙaman tarayya.
Sai dai kuma jim kaɗan bayan wannan ƙalubale da DDK ya yi wa magoya bayan Buhari, sai Bayan-Yola ya kira shi a waya, ya ce ya fita daga harkar Atiku Abubakar.
Yayin da Baban-Yola ke sheƙa wa DDK baƙaƙen kalamai, sai ya ce masa shi ba zai ci mutuncin sa ba, domin abin da ya faɗa a radiyo ra’ayi ne na siyasa. Kuma ba ya yi ba ne don ya ɓata Atiku.
Baba-Yola bai haƙura ba, sai ya fusata.
“Ko uban ka ne Lamiɗo Adamawa sai in ci …. ɗin Lamiɗo. Mu haɗu gobe, zan yi maganin ka, ko uban ka ne Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Tsaro, ka je ka kai ƙara ta a cikin Villa.
“Ka na zaune a Yola kamar yadda na ke zaune a Yola. I zan yi maganin ka. Kuma zan ci … kai da siyasar ka ɗin banza. Atiku tsarar ka ne? Ko Atiku ɗan ka ne? Zan nuna maka ina da ɗaurin gindi a ƙasar nan.” Haka Baban-Yola ya riƙa surfa wa DDK zagi.
Bayan an kama Baba-Yola, an maka shi kurkuku, inda aka caji shi da yin amfani da soshiyal midiya ya ci mutunci tare da surfa gagi, wanda ya saɓa wa dokar 2015 ta haramta yin haka da kuma Sashe na 385 da na 80 na sokar final kod.
An maka shi kurkuku babu beli. Sai 8 Ga Fabrairu za a koma domin tattauna batun beli.