Kotu dake Daejeon a kasar Korea ta Kudu ta daure wani mutum mai shekara 32 a kurkuku na tsawon shekara uku bayan an kama shi da laifin zuba ruwan sabulu a cikin ledan ruwan maganin da aka saka wa wani mara lafiya da ya kone a asibiti.
Majiya ta bayyana cewa mutumin ya aikata haka ne a wani asibiti dake Daejeon a watan Maris 2021.
“Da farko dai mutumin ya fara zuba ruwan sabulu a cikin laledan ruwan maganin sai mara lafiyan ya fada wa ma’aikaciyar jinya cewa yana fama da ciwon kirji inda hakan ya sa ma’aikaciyar jinyar ta canja ledan da igiyan ruwan magani.
“Duk da haka mutumin ya sake zuba sabulu a cikin ledan ruwan sai dai wannan karon likita ya gano cewa wasu bangarorin jikinsa basa aiki saboda sabulun ya zama guba a jikin mara lafiya.
“Zurfin bincike ya sa aka gano cewa wannan mutumin ne ke zuba ruwan sabulu a cikin ledan maganin ruwan.
Da jami’an tsaro suka kama shi sai mutumun ya bayyana cewa ya aikata haka ne a lokacin da ya yi mankas da giya sannan a nashi tunanin yana ce wai ruwan sabulu da ya zuba zai taimaka wajen wanke dattin dake cikin jinin mara lafiyan ya warke.
Jami’an tsaro sun ce wannan ba shine karon farko da mutumin ke aikata munanan laifi irin haka ba.
Discussion about this post