Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta bayyana ƙwace tulin kadarorin tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari na biliyoyin nairori.
Ƙwace kadarorin ya biyo bayan roƙon da lauyan Hukumar ICPC, Osuobeni Akponimingha ya yi wa kotun ce a ranar Laraba.
Nan take Mai Shari’a Obiora Egwuatu ya bada umarnin ƙwace kadarorin, waɗanda ICPC ta ce su na a Amurka, Abuja, Kaduna da kuma wasu wurare da garuruwa daban-daban.
Mai Shari’a ya bai wa ICPC kwanaki 60 ta Kammala binciken tabbatar da na Abdul’aziz Yari ne da ya mallaka ta hanyar satar kuɗin gwamnati.
Sannan kuma Mai Shari’a Egwuatu ya umarci ICPC ta buga sanarwa a jaridu cewa, ta na cigiyar duk wani wanda ke iƙirarin shi ya mallaki kadarorin, to ya zo ya kawo hujjojin sa, domin a ga shin na kuɗaɗen sata ne ko a’a.
An ce ICPC ta bai wa mutane wa’adin kwanaki 14. Daga nan sai kotu ta tabbatar da ƙwace kadarorin ɗungurugum.
Bayan Ƙwace Kadarorin Yari, Wata Kotu Ta Ƙwace Kadarorin Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa:
A wata sabuwa kuma, kwana ɗaya bayan ƙwace kadarorin Yari, wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ƙwace tulin kadarorin tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha.
A ranar Alhamis ce Mai Shari’a Emeka Nwedi ya bayar umarnin, bayan da lauyan EFCC ya nemi buƙatar hakan.
Kakakin Yaɗa Labarai na EFCC, Femi Babafemi ya ce daga cikin kadarorin da aka ƙwace, akwai gida mai lamba 1032 da 1033 a yankin Cadestral Zone A03, kan titin Takum da ke raɓe da babban titin Ahmadu Bello Way, Garki, Abuja.
EFCC ta zargi Okorocha da cewa da kuɗaɗen sata ya saya ko ya gida maka-makan kadarorin da ma wasu daban.
A ranar 17 Ga Janairu ce EFCC su ka maka Okorocha kotu, inda ake masa tuhuma 17, dukkan su masu nasaba da satar kuɗaɗe.
Ta na zargin sa da satar Naira biliyan 2.9 daga kuɗaɗen Jihar Imo.
Kotu ta aza ranar 12 Ga Afrilu domin komawa kotu, ranar da idan Okorocha ya kasa tabbatar da ba na sata ba ne ko aka rasa mai su, to za a ƙwace kadarorin dindindin.