ayin da ya rage saura shekara ɗaya daidai a yi zaɓen shugaban ƙasa, tuni masu neman tsayawa takarar mulkin Najeriya daga ɓangarorin manyan jam’iyyun mu biyu, APC da PDP, sun fara kartar ƙasa su na karkarwar ƙagara a fara kokawar neman samun nasara.
Manyan ‘yan siyasa tuni sun dagula matakan samun nasarar zama shugaban ƙasa a Najeriya, ta yadda su ka shigo da tsarin karɓa-karɓa, wanda su ke ganin kamar shi ne zai yi wa shiyyoyin Najeriya shida adalci.
Tarihi ya nuna irin yadda aka tsani Hausawa a ƙasar nan, ana ganin sun mamaye mulkin Najeriya. A kudancin ƙasar nan, ba a yi wa Fulanin da ke cikin gwamnati kallon Fulani, sai dai a yi masu kallon Hausawa.
To sai dai kuma shin duk da Fulani sun iske Hausawa sun danne su a sarauta, sun danne su wajen ilmi, kuma sun yi kaka-gida sun fi su shiga gwamnati, za a iya cewa Bahaushe da Bafulatani duk ɗaya ne kenan? Amsar ita ce a’a.
Tun da Najeriya ta samu ‘yanci har zuwa yau, ba a taɓa zaɓen Bahaushe ya zama shugaban ƙasa ba.
Firayi Ministan Najeriya Abubakar Yakubu, wanda aka fi sani da Abubakar Tafawa Ɓalewa, ba Bahaushe ba ne. Sunan ƙabilar su Gere. Ana ce masu Gerawa, ko kuma a kira ɗayan su Bagere. Ƙabila ce a cikin Karamar Hukumar Tafawa Ɓalewa da ke cikin Jihar Bauchi.
Janar Ironsi da ya hau mulki cikin 1966 bayan kashe su Tafawa Ɓalewa da Sa Ahmadu Bello, ɗan ƙabilar Igbo ne, asalin Jihar Abia ta yanzu.
Daga Ironsi sai kuma Janar Yakubu Gowon. Ɗan Arewa ne, amma ɗan ƙabilar Angas ne da ke cikin Jihar Filato.
Janar Murtala Mohammed Bafulatani ne kaka-da-kakanni. Domin PREMIUM TIMES Hausa ta buga wata tattaunawa da ta yi da Dakta Ibrahim Kurawa a cikin watan Agusta, 2017, inda ya kawo salsalar tsatson Fulanin da Murtala ya fito daga jinin su.
Janar Olusegun Obasanjo ya yi mulki sau biyu. Na soja da na farar hula. Shi ma Bayarabe ne daga Jihar Ogun.
Shehu Shagari da ya yi mulkin Jamhuriyar ta Biyu daga 1979 zuwa 1983, shi kuma Bafulatani ne daga Jihar Sokoto.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi mulkin soja daga 1983 zuwa 1985. Shi ma Bafulani ne. Ga shi kuma yanzu shi ne dai a kan mulkin. Ɗan Jihar Katsina ne.
Janar Badamasi Babangida da ya yi mulki daga 1985 zuwa 1993, ɗan ƙabilar Gwari ne a Jihar Neja.
Janar Sani Abacha da ya yi mulki daga 1993 zuwa 1999, ƙabilar Kanuri ne, amma haihuwar Kano.
Earnest Shonekan da ya yi riƙon ƙwarya kafin hawan Abacha, shi ma Bayarabe ne daga Jihar Ogun.
Janar Abdulsalami Abubakar, wanda ya yi riƙon ƙwarya na tsawon wata tara, shi kaɗai ne za a ce Bahaushe. Wanda kuma ya yi tarihin da ba zai taɓa kankaruwa ba. Inda ya miƙa mulki a hannun farar hula, yayin da ko shekara ɗaya bai yi a kan mulkin soja ba. Da ya ga dama da ya zarce.
Bayan Bayarabe Obasanjo ya dawo ya shafe shekaru takwas kan mulki, sai Bafulatani Umaru ‘Yar’Adua daga Jihar Katsina ya canje shi a 2007.
Goodluck Jonathan ɗan ƙabilar Ogbia, wata ƙaramar ƙabila a Jihar Bayelsa, shi ne ya hau mulki a 2010 bayan rasuwar Umaru ‘Yar’Adua.
Muhammadu Buhari ya hau mulki daga 2015, kuma yanzu sauran sa shekara ɗaya ya sauka, inda a yanzu ake ta kokawar neman mai hawa kujerar. Cikin masu kokawar kuma har yau babu tantagaryar Bahaushe ko ɗaya.
Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da zafin neman kujerar 2023, tuna ƙabilanci ya shigo cikin lamarin, ta inda Yankin Kudu maso Gabas na ƙabilar Igbo ke ganin cewa su ya kamata a bai wa mulki a APC. Hakan ya nuna ko dai a bai wa Tinubu wanda ya fidda maitar sa a fili, ko kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, wanda Bayarabe ne.
A Arewa kuwa inda Hausawa ne mafi rinjaye, ‘yan takara da dama sun fito, kuma dukkan su babu Bahaushe. Gwamna Yahaya Bello na Kogi ba Bahaushe ba ne. Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto Bafulatani ne. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Bafulatani ne. Wanda idan ya fito za a iya cewa Bahaushe ne ba Bafulatani ba, shi ne tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso.
Ko ta wane irin kallo za ka yi wa mulkin Najeriya, za ka ga cewa an maida Bahaushe ɗan turin mota kawai. Ba a bar shi ya yi shugabancin ƙasa ba, babu Hausawan asali da yawa a manyan muƙaman ministoci. Kuma babu Bahaushe Gwamna a Najeriya, a zubin gwamnonin yanzu na 2019 zuwa 2023.
A cikin gwamnonin Arewa wane ne Bahaushe? Gwamna Abubakar Bagudu na Kebbi Bafulani ne. Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto Bafulatani ne. Gwamna Aminu Masari na Katsina Bafulatani ne. Bello Matawalle na Zamfara Bafulatani ne. Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano Bafulatani ne. Gwamna. Gwamna Abubakar Badaru Bafulatani ni. Gwamnan Adamawa Bafulatani ne. To ina za mu nemi gwamna Bahaushe mu samu ne? Ku taya ni lalube a Bauchi ko Neja.
Shin lokaci bai yi ba ne da Bahaushe zai daina zama ana mulkin sa shi ba ya mulkin ne? Yayin da Fulani su ka ƙwace mulkin sarautar gargajiya a hannun Bahaushe, sun maye gurbin sa da Fulani, tun daga 1804 har yau. Sun hana Bahaushe mulki a Kano, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina da mafi yawan sauran garuruwan ƙasar Hausa.
Bahaushe bai karɓi ilmin zamani da wuri ba a Arewacin Najeriya, saboda ilmin daga hannun Turawa sai ya biyo ta hannun sarakunan gargajiya, waɗanda Fulani ne. ‘Ya’yan su ne da na sauran masu jinin sarauta aka riƙa turawa makarantun boko. Shi kuma Bahaushe ya fi bada ƙarfi a ɓangaren kasuwanci, fatauci, noma da sauran ƙananan sana’o’i.
Shi ya sa idan ka ka dubi ilmin zamani a Arewacin Najeriya, za ka ga Bahaushe na farko Musa Iliyasu da ya fara shiga Makarantar Middle ta Kano, sai a 1939 ko 1940 ya shiga. Su kuwa Fulanin jinin sarauta irin su Bello Ɗandago, tun a 1921 su ka shiga Makarantar Middle ta Kano.
Yayin da aka fara kaɗa gangar zaɓen 2023, tambayoyin su ne, shin me ya sa Bahaushe ba zai fito takarar shugabancin Najeriya ba? Me ya sa ba za a ɗauko wani Bahaushe a ce ya fito ba, kamar yadda aka ɗauko Shagari aka ce ya fito, amma da farko bai yi niyya ba?
Saboda shi tunanin Shagari a wancan lokacin, kujerar sanata ya ke hari, amma ba ta shugaban ƙasa ba.
Me ya sa ba za a ɗauko Bahaushe a ce ya tsaya takara ba, kamar yadda Obasanjo ya ɗauko Bafulatani Umaru ‘Yar’Adua, ya ce ya zo ya tsaya takara?
Shin Bahaushe bai cancanci ya riƙe Najeriya ba ne? Me ya sa Yarabawa da Igbo su ka fi Bahaushe kaifin bakin cewa ana danne su? Wa aka fi dannewa tsakanin Bahaushe da sauran manyan ƙabilun.
Ya kamata Bahaushe ya fito ya yi wa shugabannin Najeriya gori: Shin akwai mai iya cin zaɓe ba tare da ƙuri’un Bahaushe ba?
Ko kuma shi Bahaushe ba shi da amfani daga wurin jefa ƙuri’a sai wurin jagaliya?
Discussion about this post