• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    RANTSAR DA TINUBU: Kotun Koli ta yi watsi da karar rashin cancantar Tinubu shiga zaɓen 2023

    RANAR RANTSAR DA TINUBU: Za mu hana makiyaya karakaina da shanu a cikin Abuja – Shugaban Miyetti Allah

    An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka

    BA DA MU BA, TAYA ƁERA ƁARI: PREMIUM TIMES ta nesanta kan ta daga ƙungiyar da ta jona sunan ta a shirya taron karrama wasu mutane

    KIRAN RUWA: ‘Ka wa Allah ka ɗaga mana kafa, kada ka kwace mana filayen mu har 9 da ka kunno kai a kan su – Makarfi ga El-Rufai

    ‘Ni da Wike kaman ‘Yan biyu ne, muna tsage gaskiya komai dacin ta’ – El-Rufai

    SABODA TIWITA: Sanatocin PDP sun fice daga Zauren Majalisar Dattawa

    Zaɓaɓɓun Sanatocin Arewa ta Tsakiya sun nemi a ba su Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ko a-yi-ta-ta-ƙare

    KIDAYA: An kashe naira biliyan 200 wurin shirye-shiryen fara ƙidayar jama’a – Shugaban Ƙidaya

    INEC ta rantsar da Isah matsayin kwamishina a karo na biyu

    ƘAƘUDUBAR TALLAFIN FETUR: Buhari ya bukaci majalisar Dattawa ta amince masa ya tattago bashin dala miliyan 800

    AYYUKAN BAN-KWANA DA GWAMNATI: Buhari ya damƙa filin jirgin Kano da na Abuja ga Amurkawa

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

KOKAWAR 2023: Sai yaushe za a zaɓi Bahaushe ya mulki Najeriya?

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
February 26, 2022
in Rahotanni
0
KOKAWAR 2023: Sai yaushe za a zaɓi Bahaushe ya mulki Najeriya?

ayin da ya rage saura shekara ɗaya daidai a yi zaɓen shugaban ƙasa, tuni masu neman tsayawa takarar mulkin Najeriya daga ɓangarorin manyan jam’iyyun mu biyu, APC da PDP, sun fara kartar ƙasa su na karkarwar ƙagara a fara kokawar neman samun nasara.

Manyan ‘yan siyasa tuni sun dagula matakan samun nasarar zama shugaban ƙasa a Najeriya, ta yadda su ka shigo da tsarin karɓa-karɓa, wanda su ke ganin kamar shi ne zai yi wa shiyyoyin Najeriya shida adalci.

Tarihi ya nuna irin yadda aka tsani Hausawa a ƙasar nan, ana ganin sun mamaye mulkin Najeriya. A kudancin ƙasar nan, ba a yi wa Fulanin da ke cikin gwamnati kallon Fulani, sai dai a yi masu kallon Hausawa.

To sai dai kuma shin duk da Fulani sun iske Hausawa sun danne su a sarauta, sun danne su wajen ilmi, kuma sun yi kaka-gida sun fi su shiga gwamnati, za a iya cewa Bahaushe da Bafulatani duk ɗaya ne kenan? Amsar ita ce a’a.

Tun da Najeriya ta samu ‘yanci har zuwa yau, ba a taɓa zaɓen Bahaushe ya zama shugaban ƙasa ba.

Firayi Ministan Najeriya Abubakar Yakubu, wanda aka fi sani da Abubakar Tafawa Ɓalewa, ba Bahaushe ba ne. Sunan ƙabilar su Gere. Ana ce masu Gerawa, ko kuma a kira ɗayan su Bagere. Ƙabila ce a cikin Karamar Hukumar Tafawa Ɓalewa da ke cikin Jihar Bauchi.

Janar Ironsi da ya hau mulki cikin 1966 bayan kashe su Tafawa Ɓalewa da Sa Ahmadu Bello, ɗan ƙabilar Igbo ne, asalin Jihar Abia ta yanzu.

Daga Ironsi sai kuma Janar Yakubu Gowon. Ɗan Arewa ne, amma ɗan ƙabilar Angas ne da ke cikin Jihar Filato.

Janar Murtala Mohammed Bafulatani ne kaka-da-kakanni. Domin PREMIUM TIMES Hausa ta buga wata tattaunawa da ta yi da Dakta Ibrahim Kurawa a cikin watan Agusta, 2017, inda ya kawo salsalar tsatson Fulanin da Murtala ya fito daga jinin su.

Janar Olusegun Obasanjo ya yi mulki sau biyu. Na soja da na farar hula. Shi ma Bayarabe ne daga Jihar Ogun.

Shehu Shagari da ya yi mulkin Jamhuriyar ta Biyu daga 1979 zuwa 1983, shi kuma Bafulatani ne daga Jihar Sokoto.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi mulkin soja daga 1983 zuwa 1985. Shi ma Bafulani ne. Ga shi kuma yanzu shi ne dai a kan mulkin. Ɗan Jihar Katsina ne.

Janar Badamasi Babangida da ya yi mulki daga 1985 zuwa 1993, ɗan ƙabilar Gwari ne a Jihar Neja.

Janar Sani Abacha da ya yi mulki daga 1993 zuwa 1999, ƙabilar Kanuri ne, amma haihuwar Kano.

Earnest Shonekan da ya yi riƙon ƙwarya kafin hawan Abacha, shi ma Bayarabe ne daga Jihar Ogun.

Janar Abdulsalami Abubakar, wanda ya yi riƙon ƙwarya na tsawon wata tara, shi kaɗai ne za a ce Bahaushe. Wanda kuma ya yi tarihin da ba zai taɓa kankaruwa ba. Inda ya miƙa mulki a hannun farar hula, yayin da ko shekara ɗaya bai yi a kan mulkin soja ba. Da ya ga dama da ya zarce.

Bayan Bayarabe Obasanjo ya dawo ya shafe shekaru takwas kan mulki, sai Bafulatani Umaru ‘Yar’Adua daga Jihar Katsina ya canje shi a 2007.

Goodluck Jonathan ɗan ƙabilar Ogbia, wata ƙaramar ƙabila a Jihar Bayelsa, shi ne ya hau mulki a 2010 bayan rasuwar Umaru ‘Yar’Adua.

Muhammadu Buhari ya hau mulki daga 2015, kuma yanzu sauran sa shekara ɗaya ya sauka, inda a yanzu ake ta kokawar neman mai hawa kujerar. Cikin masu kokawar kuma har yau babu tantagaryar Bahaushe ko ɗaya.

Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da zafin neman kujerar 2023, tuna ƙabilanci ya shigo cikin lamarin, ta inda Yankin Kudu maso Gabas na ƙabilar Igbo ke ganin cewa su ya kamata a bai wa mulki a APC. Hakan ya nuna ko dai a bai wa Tinubu wanda ya fidda maitar sa a fili, ko kuma Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, wanda Bayarabe ne.

A Arewa kuwa inda Hausawa ne mafi rinjaye, ‘yan takara da dama sun fito, kuma dukkan su babu Bahaushe. Gwamna Yahaya Bello na Kogi ba Bahaushe ba ne. Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto Bafulatani ne. Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar Bafulatani ne. Wanda idan ya fito za a iya cewa Bahaushe ne ba Bafulatani ba, shi ne tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabi’u Kwankwaso.

Ko ta wane irin kallo za ka yi wa mulkin Najeriya, za ka ga cewa an maida Bahaushe ɗan turin mota kawai. Ba a bar shi ya yi shugabancin ƙasa ba, babu Hausawan asali da yawa a manyan muƙaman ministoci. Kuma babu Bahaushe Gwamna a Najeriya, a zubin gwamnonin yanzu na 2019 zuwa 2023.

A cikin gwamnonin Arewa wane ne Bahaushe? Gwamna Abubakar Bagudu na Kebbi Bafulani ne. Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto Bafulatani ne. Gwamna Aminu Masari na Katsina Bafulatani ne. Bello Matawalle na Zamfara Bafulatani ne. Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano Bafulatani ne. Gwamna. Gwamna Abubakar Badaru Bafulatani ni. Gwamnan Adamawa Bafulatani ne. To ina za mu nemi gwamna Bahaushe mu samu ne? Ku taya ni lalube a Bauchi ko Neja.

Shin lokaci bai yi ba ne da Bahaushe zai daina zama ana mulkin sa shi ba ya mulkin ne? Yayin da Fulani su ka ƙwace mulkin sarautar gargajiya a hannun Bahaushe, sun maye gurbin sa da Fulani, tun daga 1804 har yau. Sun hana Bahaushe mulki a Kano, Sokoto, Zamfara, Kebbi, Katsina da mafi yawan sauran garuruwan ƙasar Hausa.

Bahaushe bai karɓi ilmin zamani da wuri ba a Arewacin Najeriya, saboda ilmin daga hannun Turawa sai ya biyo ta hannun sarakunan gargajiya, waɗanda Fulani ne. ‘Ya’yan su ne da na sauran masu jinin sarauta aka riƙa turawa makarantun boko. Shi kuma Bahaushe ya fi bada ƙarfi a ɓangaren kasuwanci, fatauci, noma da sauran ƙananan sana’o’i.

Shi ya sa idan ka ka dubi ilmin zamani a Arewacin Najeriya, za ka ga Bahaushe na farko Musa Iliyasu da ya fara shiga Makarantar Middle ta Kano, sai a 1939 ko 1940 ya shiga. Su kuwa Fulanin jinin sarauta irin su Bello Ɗandago, tun a 1921 su ka shiga Makarantar Middle ta Kano.

Yayin da aka fara kaɗa gangar zaɓen 2023, tambayoyin su ne, shin me ya sa Bahaushe ba zai fito takarar shugabancin Najeriya ba? Me ya sa ba za a ɗauko wani Bahaushe a ce ya fito ba, kamar yadda aka ɗauko Shagari aka ce ya fito, amma da farko bai yi niyya ba?

Saboda shi tunanin Shagari a wancan lokacin, kujerar sanata ya ke hari, amma ba ta shugaban ƙasa ba.

Me ya sa ba za a ɗauko Bahaushe a ce ya tsaya takara ba, kamar yadda Obasanjo ya ɗauko Bafulatani Umaru ‘Yar’Adua, ya ce ya zo ya tsaya takara?

Shin Bahaushe bai cancanci ya riƙe Najeriya ba ne? Me ya sa Yarabawa da Igbo su ka fi Bahaushe kaifin bakin cewa ana danne su? Wa aka fi dannewa tsakanin Bahaushe da sauran manyan ƙabilun.

Ya kamata Bahaushe ya fito ya yi wa shugabannin Najeriya gori: Shin akwai mai iya cin zaɓe ba tare da ƙuri’un Bahaushe ba?

Ko kuma shi Bahaushe ba shi da amfani daga wurin jefa ƙuri’a sai wurin jagaliya?

Tags: BahausheLabaraiNajeriyaNew
Previous Post

‘YAN BINDIGA SUN KADE: Za mu siyo Jiragen da ake tuka su da na’ura mu aika su dazuka su gama da ‘yan bindiga – El-Rufai

Next Post

DAJIN DA AKA KETO KAFIN BUHARI YA SA WA DOKAR ZAƁE HANNU: Shugaban Ƙasa ya sake gano wani giɓi a zubin haƙoran Sabuwar Dokar Zaɓe

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Gwamnatin Buhari ta bada kwangiloli 878 daga 2015 zuwa 2021 -Boss Mustapha

DAJIN DA AKA KETO KAFIN BUHARI YA SA WA DOKAR ZAƁE HANNU: Shugaban Ƙasa ya sake gano wani giɓi a zubin haƙoran Sabuwar Dokar Zaɓe

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • TASHIN HANKALI A FILATO: Miyetti Allah sun yi kururuwar Jasawa na shirin kakkaɓe su ƙarƙaf, an kwashe masu shanu 25,000 cikin mako biyu
  • SUN CI TALIYAR ƘARSHE: Sanata Lawan ya damu ganin kashi 70 bisa 100 na ‘Yan Majalisa sun faɗi zaɓe
  • RIGIMAR SHUGABANCIN MAJALISA: ‘Ina goyon bayan Abbas, shi zan yi wa kamfen wurjanjan’ – Wike
  • RASHIN SANI: Yadda jami’an Kwastam suka bindige ɗan uwansu Jami’i a shingen bincike
  • WALLE-WALLE DA RAYUKAN ZAMFARAWA: Yadda ilmi ya taɓarɓare, talauci ya ƙara katutu, mace-macen ƙananan yara ya yi muni a mulkin Matawalle

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.