Jagoran APC Bola Tinubu ya zabura, inda ya yi gaggawar maida raddi kan labarin da kafafen yaɗa labarai su ka ɗauka, yayin ziyarar da ya kai wa sabon Olubadan na Ibadan, Lekan Balogun a gidan sa na Ibadan.
Kafafen yaɗa labarai sun ɗauki rahoton NAN, inda aka ruwaito Jagaban na cewa zai iya yin kokawa da alade.
Sai dai kuma a cikin martanin da Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Tunde Rahman ya fitar, ya bayyana cewa ba haka Tinubu ke nufi ba.
Ya ce ɗan takarar bai ce zai iya yin kokawa da alade ba, amma ya yi wata karin magana mai kama da zaurance.
“Tinubu zaurance ne ya yi, inda ya ce, “Na karanta abin da wani falsafa ya rubuta cewa: “Duk wanda zai yi kokawa da alade, to ya shirya da sanin cewa jikin sa zai ɓaci da kashin alade.”
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin, inda Tinubu ya ce “babu wata barazana ko sharrin da zai iya yi min katanga da zama shugaban ƙasa. Saboda haka na shirya kafsawa. Na karanta inda wani falsafa ya ce, wanda ya ce zai yi kokawa da alade, to ya sani sai ya ɓata jikin sa da datti. To ni na shirya ɓata nawa jikin da datti.”
Tinubu A Ziyarar Olubadan Na Badun:
‘Babu wata barazana ko sharrin da zai min katanga da kujerar shugaban ƙasa -Tinubu:
Jagoran APC kuma mai neman tsayawa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa babu wani sharri, tuggu ko barazanar da za su iya dakatar da shi daga mafarkin sa na zama shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Tinubu ya yi wannan kakkausan kalaman ne a ranar Lahadi, a yayin da ya kai ziyara fadar zaɓaɓɓen Basaraken Badun, Olubadan na Badun, Lekan Balogun.
Tinubu ya kai masa ziyarar ce a gidan Balogun ɗin da ke Badun, a unguwar Alarere.
Ya kai ziyarar ce a matsayin neman tubarrakin Olubadan a kamfen din da Tinubu ɗin ke yi na neman a tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Bayan ya shafe dogon lokaci ya na rara-gefe, a ƙarshe dai Tinubu ya ayyana neman tsayawa takarar sa, bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Ƙasa.
Ya shaida wa manema labarai cewa ya daɗe ya ke da muradin neman zama shugaban ƙasa.
Ba Wanda Ya Isa Ya Yi Min Barazana Ko Sharrin Hana Ni Zama Shugaban Ƙasa:
“Duk lokacin da batun takarar Bayarabe ta bijiro, sai a kama wasu maganganu da surutai da gutsuri-tsoma.
“Sai a kama kame-kame, amma ana jin tsoron a fito gaba-da-gaba a Tunkari Zakin Bourdilon.” Inji Tinubu.
Daga nan ya ce shi fa a shirye ya ke, babu wata barazana ko sharrin da zai iya hana shi neman kujerar shugaban ƙasa.
“Na fito na shirya zama Shugaban Najeriya, babu wanda ya isa ya hana ni.”
Kujerar Shugaban Ƙasa 2023: Na Shirya Yin Rigima Ko A Cikin Dagwalon Kwatami -Tinubu:
“Kai ni fa na karanta ra’ayin wani falsafa, wanda ya rubuta cewa, “wanda ya ce zai yi kokawa da alade, to kuwa ya sani jikin sa zai yi kaca-kaca da datti. To ni na shirya yin faɗan, kuma na amince jiki na ya yi kaca-kaca da datti da warin alade.”
Tinubu Kaɗai Ke Da ‘Laƙanin’ Iya Gyaran Najeriya -Sanwo-Olu:
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu ya nuna cewa jagoran APC Bola Tinubu kaɗai ya ke goyon baya a cikin masu takardar neman tsaya wa APC zaɓen 2023.
A ranar Juma’a ce ya bayyana cewa Tinubu wanda shi ma ya taɓa yin gwamna na jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, shi kaɗai ne a cikin masu neman tsayawa takara ke da abin da ya kira “laƙanin iya gyara Najeriya”.
Da ya ke magana a wurin taron haɗa-ka na Kwamishinoni da ‘Yan Majalisar Jihar Lagos, Sanwo-Olu ya ce Tinubu ya na da dukkan wasu sabubban cancantar ya mulki Najeriya, kuma idan ya zama shugaba, ko shakka babu zai iya maida ƙasa tsaba.
“Ya kamata mu tafi tare, musamman ganin yadda zaɓen 2019 ya gabato. Ina yin kira a gare mu baki ɗaya mu taru mu haɗa kai mu goyi bayan takarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen fidda-gwani na APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
“Ya yi wa al’ummar Jihar Legas dukkan wani abin da zai iya yi. To a yanzu ya na so ya yi wa Najeriya gyara kamar yadda ya gyara Legas ta samu gagarimin ci gaba.
“Tinubu ne mutumin da ya fi cancanta ya mulki Najeriya. Saboda ya san matsalolin da su ka addabi ƙasar nan sosai, kamar yadda yadda ya san bayan hannun sa. Kuma ya na da laƙanin da zai yi amfani da shi ya yi gyaran Najeriya.” Inji Sanwo-Olu.
Sanwo-Olu dai shi ne Tinubu ya bai wa takarar gwamnan Legas a zaɓen 2019, bayan ya hana gwamnan lokacin, Akinwunmi Ambode tsayawa takara karo na biyu, domin ya yi tazarce.
Bisa dukkan alamu Tinubu na iya samun tirjiya daga jihohin Kudu maso Yamma, ganin yadda wasu suka tashi haiƙan dare da rana su na buga wa Matakimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo gangar ya fito takara shi ma.
Discussion about this post