Daga cikin masu azarɓaɓi, gaggawa da zaramboton saurin fitowa takarar zaɓen 2023, wanda saura watanni 12 daidai a kaɗa ƙuri’a, Atiku ne ya fi saura yawan jaraba sa’a, kuma ya sha ganin samu ya ga rashin nasara a zaɓuka daban-daban.
Atiku Jonathan ya kayar zaɓen fidda-gwanin 2011. A zaɓen 2015 Atiku ya taimaka wa Shugaba Buhari ya ci zaɓe, sannan kuma a 2019 ya gwabza tare da Buhari, amma bai yi nasara ba.
Babbar matsalar da Atiku zai iya fuskanta ita ce rashin tantagaryar masu kishin jefa masa ƙuri’a. Amma don jama’a, Atiku ya na da jama’a. Kawai dai jama’ar da za su iya yi masa ruwan ƙuri’u ne ba shi da su.
Wannan matsalar kuwa ta fito fili ne a zaɓen 2019, musamman inda a Kano inda aka yi tunanin zai iya samun ƙuri’u kusan miliyan biyu, sai ya tashi da yawan waɗanda ba su ma kai adadin da ya samu a wasu ƙananan jihohi ba.
Atiku na samun tangarɗa a kamfen ɗin sa, ta hanyoyi da dama. Kaɗan daga cikin su akwai bada fifiko ko maida hankali kan yankin kudu wajen al’amurran masu tafiyar da kamfen ɗin sa. Ko a wannan shekarar Wazirin Adamawa ya ɗora ɗan kudu, Remind Dokpesi mai gidan talbijin na AIT a matsayin Daraktan Kamfen.
Mutane da dama na ganin kamata ya yi Atiku ya fito kawai gaba-gaɗi ya yi daraktocin kamfen biyu, wato ɗaya kudu, ɗayan kuma a Arewa.
Atiku na da matsala a siyasar rama bugun yarfen siyasa a Arewa. Hakan ya faru a zaɓen 2023, inda a Arewa aka riƙa aibata shi da yi masa yarfen siyasa daban-daban, amma babu zaratan sojojin baka a soshiyal midiya da za su riƙa rama masa sharri, yarfe da jagaliyanci da buyagin da aka riƙa yi masa.
Don sai da ta kai har a wurin zaɓe a ranar zaɓe ana bin sa da yarfen cewa “kada a zaɓi wanda ya ce zai sayar da NNPC.”
Tun daga ranar da Atiku ya ce zai sayar da NNPC a lokacin kamfen ɗin 2019, shi bai fito ya yi wa talakawa bayani dalla-dalla abin da ake nufi da sayar da NNPC ba. Sannan kuma dakarun kamfen ɗin sa da sojojin bakan sa ba su yi yaƙin wayar wa talakawan Arewa kai dangane da abin da ake nufi da ‘sayar da NNPC ba.’
Wannan ya bada wawakeken giɓin da masu adawa da shi su ka yi amfani su na yi masa yarfe, ana fassara shi da cewa mutanen sa zai sayarwa, sannan ya kewaya ya saye daga hannun su.
Wata matsala da Atiku ke fuskanta ita ce wasu da ke kewaye da shi ba ka ganin su a jikin sa sai kakar siyasa ta zo. Za su kewaye shi su hana mashawarta na ƙwarai su matsa ballantana su ba shi shawara ta gari.
Sannan akwai ‘yan ‘idan ta yi ruwa rijiya, idan ba ta yi ba masai’, masu ƙoƙarin samun na watsawa aljihu a duk lokacin da tafiyar kamfen ɗin Atiku ta kunno kai. Wasu na ƙoƙarin azurta kan su ta hanyar kamfen ɗin, ta yadda ko an faɗi zaɓe, to ba ta ɓare da su ba.
A zaɓen 2019 matasa da dama a Arewa musamman ‘yan soshiyal midiya masu kare shi, sun watsar ganin yadda ya fi mayar da hankali kan murna da samun wani matsashin soshiyal midiya daga Kano, wanda ya canja sheƙa ya koma ɓangaren sa. Sai dai kuma matashin ya gwasale Atiku, domin bai jima tare da shi ba, ya sake komawa cikin gonar da ya fito.
Wasu da dama na cewa Atiku bai fitar da kuɗi a kamfen ɗin sa na 2019 ba, kamar yadda aka yi tsammanin zai yi. To ko ma dai me kenan, wannan ce damar Atiku ta ƙarshe, matsawar shi PDP ta tsayar a matsayin ɗan takarar su a 2023.
Akwai jan aiki ga jagororin tafiyar Atiku, ko da kuwa shi ɗin ne PDP ta tsayar. A Arewa inda a nan ne aka fi samun ƙuri’un da ke kai ɗan takara ko jam’iyya cin zaɓe, siyasar ta sauya tun daga 2011, inda a yanzu addini da malaman addini na da tasiri kan masu jefa ƙuri’a. Yanzun nan sai a hau mimbari a yi biji-biji da ɗan takara, ko da kuwa babu wata ƙwaƙƙwarar hujjar yin hakan.
Malamai da dama sun fito fili su na nuna ga ɗan takarar da su ke so. Don haka akwai jan aiki ga jiga-jigan kamfen ɗin Atiku domin sanin makamar yadda za su tunkari yarfen siyasa da watsa ji-ta-ji-tar da akan yi a Arewa, kan ɗan takarar da ba shi wasu gungun ba’arin masu faɗa-a-ji ke so ya yi nasara ba.
Wannan jan aiki kuwa a gaskiyar magana, ya fi ƙarfin Dokpesi, Babban Daraktan Kamfen ɗin Atiku. Domin mutumin da tun tafiya ba ta yi nisa ba ya ke iƙirarin zai iya tuɓewa zigidir a bainar jama’a, maganar gaskiya ba irin sa ne zai ciwo wa ɗan takarar dandazon dubun-bubatar ƙuri’un matan auren Arewa ba ne. Ko dai Waziri ya tashi tsaye ya sauya takalmin bugun fenaritin sa na ƙarshe, ko kuma ya ɗinke inda takalmin ya yage tun kafin alƙalin wasa ya ba shi umarnin buga ƙwallon a 2023.
Discussion about this post