Shari’ar waɗanda ake zargi da yin garkuwa, sannan da kashe Hanifa Abubakar mai shekaru biyar ta samu tsaiko, saboda rashin samun lauyoyin da za su tsaya masu a kotu.
Waɗanda ake zargin da suka haɗa da Abdulmalik Tanko da wasu mutum biyu, an zarge su da yin garkuwa da kuma kashe Hanifa cikin watan Disamba.
Abdulmalik Tanko, Hashimu Isyaku da Fatima Jibrin sun bayyana a Babbar Kotun Kano, mai lamba 6, a gaban Mai Shari’a Usman Na-Abba.
An caji su ukun da aikata laifukan haɗa baki su aikata laifi, yin garkuwa, ɓoye wanda suka yi garkuwa da shi, aikata kisan-gilla, laifukan da Mai Gabatar da Ƙara ya ce sun saɓa wa Sashe na 97, na 274, na 277 da kuma na 221 na dokar Finel Kod.
Sai dai a ranar Litinin ɗin nan ne aka gurfanar da su, amma babu lauyoyin da za su kare su daga tuhumar da ake yi masu.
Daga nan sai Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, kuma Antoni Janar na Jihar, M.A Lawal, ya roƙi ko za a iya ci gaba da shari’ar duk kuwa da cewa waɗanda ake tuhuma ɗin ba su da lauyoyi masu kare su.
Daga nan sai Mai Shari’a Na-Abba ya tambayi waɗanda ake zargin ko za su samo lauyoyi su kare su? Ko kuwa za gwamnatin jiha ta samo masu masu kare su?
Tanko wanda shi ne babban mai laifin ya ce shi ba zai iya ɗaukar lauya ba, amma ya yarda jiha ta samo masa. Su ma sauran su ka zaɓi hakan.
Daga nan sai Antoni Janar ya roƙi kotu a ɗage shari’ar zuwa ranar 14 Ga Fabrairu, inda kafin ranar Gwamnatin Jihar Kano za ta samo masu lauyoyin da za su kare su.
Daga nan Mai Shari’a Na-Abba ya amince, ya ce a koma kotu ranar Litinin, 14 Ga Fabrairu.
Discussion about this post