Kotun majistare dake kusa da tashar jiragen saman Aminu Kano dake jihar Kano ta yanke wa wata dillaliyar kayan mata Sadiya Haruna hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni shida bayan an kamata da laifin bata wa shahararren dan fina-finan Hausa Isah Isah suna.
Sadiya wacce ita ma tsohuwar ‘yar fim ce ta bata wa Isah suna a wani bidiyo da ta saka a shafinta ta Twitter a yanar gizo.
Bisa ga labarin da ‘Daily Nigerian’ ta buga an nuna cewa a bidiyon Sadiya ta ce da ita da Isah sun yi aure na dan wani lokaci kuma a wannan lokacin da take matsayin matarsa, Isah ya rika saduwa da ita ta dubura da karfi da tsiya.
An fara gurfanar da Sadiya a shekaran 2019 a kotu saboda zargin kazafin da ta yi wa Isah a wannan bidiyon. Wannan abinda ta aikata ya sabawa sashe na 391 na penal code.
A ranar Litini ne alkali Muntari Dandago ya yanke ya Sadiya hukuncin zama a kurkuku na tsawon watanni shida.
Hukuncin da Dandago ya yanke ya biyo bayan hukuncin da alkalin kotun shari’a Ali Danzaki ya yanke wa Sadiya na shiga makarantar islamiya na Darul Hadith dake kwatas din Tudun Yola a Kano na tsawon watanni shida.
Danzaki ya ce Sadiya za ta rika zuwa islamiyan tare da sa idon jami’an hukumar Hisbah dake jihar.
Zuwa yanzu Sadiya ta kammala hukuncin da Ali ya yanke mata bayan ta amsa laifinta a gaban Danzaki.
Discussion about this post