Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
Bincike ya nuna cewa babu abinda yake lalata jikin dan Adam, ya rugurguza shi, yayi masa illa, ya kanjame, cutuka su kama shi, kamar damuwa. Idan damuwa tayi yawa ta kan jawo ciwon hawan jini, ta kan hana cin abinci ma, sai ka ji baka damu ba, sai ka ji kana koshe, wato ka ji baka jin yunwa, alhali kuwa da babu damuwar, da sai kasan cewa akwai yunwa a tare da kai.
Hanyoyin damuwa suna da yawa, ya danganta da irin jarabawar kowa ne mutum. Sai dai akwai damuwar da ta ke ta shirme, maras ma’ana, mai muni.
Allah Ta’ala yakan jarabci bayin sa da wasu abubuwa a cikin wannan rayuwa ta duniya, domin ya daukaka matsayin su, ko domin ya gwada karfin imanin su, ko kuma domin su kara samun kusanci da shi (Allah). Misali, akwai rashin lafiya, akwai mutuwa, akwai tawayar arziki/karayar aziki ko talauci, akwai samun jarabawa cikin ‘ya’ya, akwai tashe-tashen hankula da rashin tsaro da rashin zaman lafiya, da sauran su. Irin wannan jarabawa, babban maganin ta shine, na farko yin hakuri, da kamewa, da komawa zuwa ga Allah domin ya yaye wannan damuwa, da bin duk hanyoyin da suka dace, na Shari’ah, domin kawo karshen damuwar!
Damuwa maras ma’ana kuwa, wadda kai ne kake sa kanka cikin ta, misali, nisantar Alkur’ani mai girma, hadama (greed), nisantar Sallar dare, yiwa bayin Allah girman kai, zama da mutanen banza, rashin tsayar da adalci da zaluntar mutane, yin karya da aiwatar da rashin gaskiya, damuwa akan lamarin wani, damuwa sanadiyyar yiwa wani hassada saboda Allah ya daukaka shi, damuwa saboda jin haushin mutane, idan kuma da za’a ce me yasa kake jin haushi wane, sai kace “ban sani ba”, damuwa akan munanan zato, damuwa akan kudurin daukar fansa, bibiyar bayin Allah da bin diddigi.
Wannan duk nau’ukan damuwa ne da Dan Adam yake sa kansa a ciki, ya sani ko bai sani ba. Kuma irin wannan nau’uka na damuwa da daman su babu abinda suke janyo wa Dan Adam sai ci baya, da dawwama cikin bakin ciki, wanda kuma barin su shine kubuta da samun hutun zuciya da samun ci gaba cikin rayuwa, da samun kwanciyar hankali.
Kada ka yarda da duk wani abun da ba zai amfanar da kai ba ya sami gurin zama cikin zuciyar ka. Kayi sauri ka kau da shi ka nemi tsarin Allah da kiyayewar sa. Ka sani, a koda yaushe, abinda yake kai komo gare ka na damuwa ba zai taba canza nufin Allah ba, abinda Allah yaso kaddarawa a kanka shine yake faruwa. To don me zaka bar zuciyar ka tayi ta kai komo akan abin da ya faru, ko kake tsoron faruwar sa, ko bai ma faru ba?
Sannan ka sani, rayuwar ka tana cike da yawan nazari, idan ya zamanto abinda yake kai komo a gare ka, cikin zuciyar ka, wanda zai amfane ka ne, a cikin addinin ka da rayuwarka, ba shakka kayi dace a cikin rayuwarka. Duk lokacin da wani tunani yazo maka, kafin ka bari yayi tasiri a cikin zuciyar ka, to, fara gwada shi, shin zai amfanar da kai cikin addini da rayuwa..?
• Maganin yaye dukkanin damuwa, da maganin cututtukan zuciya
Yahya Bin Mu’az Allah ya kara masa rahama yana cewa:
“Maganin duk wata damuwa da duk wata cuta dake cikin zuciya tana cikin abubuwa guda biyar;
1. Karatun Alkur’ani tare da hakaito ma’anoninsa.
2. Rashin cika ciki da abinci (yana ishara zuwa ga yawaita azumi).
3. Sallar dare.
4. Kankan da kai lokacin da gari ya waye (ishara zuwa ga tawadu’u da rashin girman kai ga bayin Allah).
5. Zama da mutanen kirki.” [Duba Almajmu’, mujalladi na 2, shafi na 407]
Ina rokon Allah Ta’ala ya kara muna hutun zuciya, ya bamu rayuwa mai albarka, ya sanya mu cikin bayin sa wadanda zai yi alfahari da su ranar Alkiyama, ya jiƙan iyayen mu da dukkan magabatan mu, amin.
Imam Murtadha Muhammad Gusau, 08038289761
Discussion about this post