A yayin da aka soma kada gangar siyasa domin shiga kakar zaben shekara ta 2023, dukkanin alamu na nunawa lisaffin siysar bana ma a wajen nemawa Jigawa sabon ango, ba’a maganar mutanen Jigawa-ta-Gabas wato Hadejiawa, duk da kaifin sunan mutanen Hadejia da sukayi wajen cigaban Jihar Jigawan.
Hadejia ko Hadejia Emirate ita ce Senetoriya ta Jigawa-Arewa-maso-Gabas, mai Kananan-Hukumomi takwas. A tarihin siyasar wannan lokacin tun daga kirikiro Jahar kawo yau wannan yankin ne kadai bai taba jagorancin Jigawa ba. Kuma dukkan alamu na nunawa a wannan karonma za a kuma.
Hadejia ita cibiyar tattalin arzikin Jahar Jigawa, yankin ne ke bada sama da kashi saba’in (70%) na arzikin da Jigawa ke samarwa a cikin gida, yankin Hadejia ne yafi kowa ne yanki noma Ridi da Soborodo a fadin Arewacin Nijeriya, Yankin Hadejia ne ke kan gaba wajen noman shinkafa a Nijeriya. A takaice tattalin arzikin Jihar Jigawa wanda ya taállaka da noma, kusan akasarin noman ana yi ne a wannna yankin. Kasuwar kifi da sauran Naman-Uuwa babu irin wannan kasuwar a fadin Arewa-maso-Yamma cin Nijeriya. Amma har yau mutanen wannan yankin an ki aminta da su wajen bada tasu gudun mawar a jahar Jigawa. Abin tambaya shin mai nene zunubinsu?
Fada da rashin cikawa, labarum fuska ya banbanta da na zuciya duka ba komai bane a halayen siyasar Nijeriya. A takiataccen bincike na akan muámala Bahadejie da abokan zaman sa musamman a cikin jahar Jigawa, mafi akasarin mutane sun nuna mutane ne masu kawaici, kuma sukan hana nasu su bawa bare, ba wai don basa son nasu ba, kawai don nuna kawaici. Shin suna da kyama? A kasarin mutane sun nuna basu da kyama, suna da son koya wa duk abokan aikin su ko na kasa da su aiki da ilimin da suke da shi. Hakuri da iya muámala yasa suke da alaka da dukkanin manya a jahar jigawa dama kasa baki daya.
Duk jagororin siyasar Jihar Jigawa a jiya da yau, dukka su na tunkaho ne da mutanen wannan yankin wajen zame musu dakarai don cimma burin siyasar su, kuma su kan aminta da su harma su zamanto masu fidda su kunya, a yayin da ake bukatar nagartattun mutane walau a tarayya koma a wajen tarayya. To me nene zunubinsu nakin amince wa da su wajen jagorar jigawa don bada tasu gudun mawar.
A misali, Malam Sule Lamido a matsayin sa na babban jagoran PDP, a tsawon lokacin da PDP tayi tana mulki tsakanin 1999 zuwa 2015, mutane bakwai (7) da suka zamanto Ministoci daga Jigawa guda biyar (5) daga cikinsu duka sun fito ne daga yankin Hadejia. A lokacin mulkin Malam Sule Lamido, ya yi alfahari da irin gudun mawayar da mutannen yankin nan suka bashi wajen samun nasara a mulkin da yayi dama cigaban jamaíyar su ta PDP. Amma ita jamaíyar PDPn a shekarar 2007, 2015 da 2019 sun juya wannan yankin baya, wajen basu damar yin takara a jamaíyar, wannan mataki na PDP bisa jagoran cin Sule Lamido ya bawa kowa mamaki, duk da cewar a yankin ne yafi ko ina magoya baya da ma dakaran siyasa da yake alfahari da su, wayanda har kawo yau suna tare da shi.
Har a wannan lokacin da aka soma kadawa na nuna alama cewa a wannan karon ma babu lissafin yankin Hadejia a takarar PDP, tun da alamu ya nuna, har masu baki da kunu ma sun zurbaba wajen bayyan mai yiwa jamaíyar takare a shekara mai zuwa, duk da cewa jamaíyar na da fittatun mutane kuma kwararru yan siyasa da ya kamata su jira lokaci kafin yanke hukunci. Wannan na nuni da cewa har yanzu babu ma tunanin wannan yankin a gaban su. Ko menen zanubin wannan yankin na kokarin har abada hana su takara a wannan jamaíyar.
Koda shima Maigirma Gwamna Mohammad Badaru Abubakar ya sake tabbatar da da kusancin sa, muamalar sa da kuma kawaicin mutanen wannan yankin da irin gudunmawar da suke ba shi da ma nuna masa kauna, a yayin da wata kungiya take martaba shi a garin Hadejia, wanda ya tabbatar da cewa babu wani gwamnan da ya samu karbuwa a wajen mutanen Hadejia kamar shi.
Badaru ya sake tabbatar da irin kishin kasa da alúmmar wannan yankin da kuma sadaukar war su, ya nuna cewa tun da ya ke a gwamna babu kungiya daga wannan yankin da taje masa da biyan bukatar kan su sai dai maganar a yi wa kasa da talakawa aiki, wanda wannan yunkuri ne na gyara kayan ka, wanna ya taimaka masa wajen gina Jihar Jigawa.
To amma ita ma da alama kalangun da ake kadawa don taka rawa a APC, yana nuna alamun shirin kamar na jiya ne, harsashe na nunawa da kyar in an bawa mutanen wannan yankin damar taka tasu rawar, kuma hakan ba zai zo da mamaki ba yadda baki ya nuna yadda yake neman karkata.
To, koda suma sauran al’umma Jigawa, wanda kowa ya aminta da cewa ana zaman lafiya da juna, kuma ci gaban jahar mu a yau ya fi jiya. Shin wane hange suke game da yadda wannan yankin na samu irin wannan matsayi, marar dadi. Shin kuwa bai zamanto abin tambaya ba zahirin aminci, yarda da juna, zamantakewar ta gaskiya a tsakanin mutanen wannan jaha ba. Shin wane irin zunubi wannan yankin yayi ta yadda sauran yan uwansa ba za su goya masa bay aba wajen bada gudun mawar su wajen gina wannan jaha.
Jahar Jigawa mai al’ummah iri daya, addini daya kuma yan uwan juna, adalci shine kadda a kafa ginshikin banbanci da wariya ga wani yankin don biyan bukatar wasu mutane kalilan.
Allah ya raya mana jahar Jigawa.
alhajilallah@gmail.com