Hukumar shirya jarabawar WACE ta bayyana cewa kashi 48.61% na dalibai ne suka yi nasarar cin darussa 5 da suka hada da Lissafi da Turanci a jarabawar GCE na 2021.
Shugaban hukumar Patrick Areghan ya sanar da haka ranar Litini.
Areghan ya ce an fara rubuta jarabawar ranar 12 ga Nuwamba aka kammala ranar 22 ga Disemba 2021. Dalibai 51,444 daga cikin dalibai 52, 973 da suka yi rajista suka rubuta jarabawa.
“Dalibai 25,008 ko kuma dalibai kashi 48.61 ne suka yi nasara a jarabawar inda a cikin darussan da suka yi nasara akwai Lissafi da Turanci. A cikin su akwai maza 12,272 da mata 12,736.
” Dalibai 32,637 suka ci kiredit a darussa biyar banda Turanci ko Lissafi. A cikin su akwai maza 15,832 da mata 16,805
Ya ce hukumar ta samu karin kashi 8.79 na daliban da suka yi nasara a jarabawar a shekaran 2021 fiye da shekarar 2020.
Areghan ya ce dalibai 3,968 hukumar ta rike sakamakon jarabawar su saboda laifin satar ansa.
Daga nan Areghan ya ce hukumar ta yi shiri tsaf domin ganin daliban da basu da lanban katin dan ƙasa NIN sun rubuta jarabawar a shekarar 2022.
Bayan haka shugaban hukumar ya ce nan gaba dalibai za su iya samun satifiket din jarabawar ta yanar gizo.
Aregrhan ya ce hukumar ta yi haka ne domin kama masu yin satifiket din jarabawar na karya.
Discussion about this post