Duk da dambarwar cikin gida da ya tirnike ƴan takara biyu da kowa ke ikirarin shine halastaccen ɗan takarar jam’iyyar APC a zaben shugaban hukumar gundumar Abaji dake Abuja, Jam’iyyar ce ta yi nasara a zaɓen.
Malamin zaɓe Gabriel Mordi, ya bayyana cewa ba za a iya faɗin ko wanene yayi nasara cikin mutum biyu dake kalubalantar juna a kotu ba, jam’iyyar APC ɗin ce ta yi nasara a zaɓen sai dai sai an jira hukuncin kotu
APC ta kwashi zunzurutun kuri’u har 7,280 inda ɗan takaran PDP Hahaha Garba ya samu ƙuri’u 4,063.
Mordi ya ce za a jira kotu ta yanke hukuncin ainihin ɗan takaran jam’iyyar APC cikin mutum biyu da jani-in-jaka kan kujerar.