Gamayyar rundunonin ‘yan sanda da sojoji sun ceto mutum 32 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a jihar Zamfara.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya bayyana a hedikwatar ‘yan sanda dake Gusau.
Shehu ya ce jami’an tsaron sun gano cewa mutanen da aka yi garkuwa da su mazauna jihohin Niger, Katsina, Kebbi da Zamfara ne.
Ya ce an kai mutanen asibiti sannan har an maida su garurruwan su.
Shehu ya ce mutum 10 daga cikin daga cikin su an sace su ne a hanyar Sheme zuwa Funtuwa ranar Alhamis.
“A ranar 26 ga Janairu ‘yan sanda dake sintiri a hanyar Mada sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su a hanyar Sheme zuwa Funtuwa jihar Katsina.
“An yi garkuwa da wadannan mutane yayin da suke hanyar zuwa karamar hukumar B/Magaji daga jihar Legas ranar 10 ga Janairu.
“Mutum biyu daga cikinsu ‘yan asalin jihar Kaduna ne daya dan jihar Kebbi.
“A ranar 30 ga Janairu rundunar sojin Najeriya ta ceto mutum 19 da a ciki akwai maza 15 da mata hudu da suma anyi yi garkuwa da su a Dansadau dake karamar hukumar Maru.
“An gano cewa an yi garkuwa da mutanen yayin da suke aiki a gonakinsu ne. Sai da suka shafe watanni biyu tsare hannun ‘yan bindiga kafin suka kubuta.