Wata ƙungiyar ƙabilar matan Igbo mai suna Igbo Women Forum, ta ce za ta shiga ta fita har sai ta tattara kan mutum miliyan 25 da za su jefa wa Gwamna Yahaya Bello ƙuri’u, a zaɓen 2023.
Ƙungiyar ta sha wannan alwashin a Abuja, a cikin wata sanarwar da Shugabar Kungiya Uju Obi ta sanya wa hannu.
“Ƙungiyar mu za ta shirya gagarimin gangamin taro a Abuja, domin tabbatar da an samu adadin yawan mutanen, kuma su nuna goyon bayan Yahaya Bello.
Yayin da ta ke jero ‘karamomin’ Yahaya Bello, Obi ta ce Gwamnan ya ce idan ya zama shugaban ƙasa, babban abin da zai fi maida hankali a kan matsalar tsaro.
“Bello ya nuna shi ne zaƙaƙurin da zai iya daƙile matsalar tsaro da ta haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran manyan laifukan da suka addabi ƙasar nan.
“Wani abin birgewa ga Yahaya Bello shi ne yadda ake son shi a kowane sashe na faɗin ƙasar nan. Sannan kuma ba shi da ƙabilanci ko addinanci a siyasar sa.
“Wannan kuwa ba wani abin mamaki ba ne, domin ya nuna rashin ƙabilanci a gwamnatin sa ta jihar Kogi, saboda ya rungumi kowace ƙabila.”
Obi ta ce a matsayin Bello mai shekaru 46 da haihuwa, za a iya cewa ya na wakiltar wani sabon sauyin yanayin siyasar da za a damƙa akalar riƙon ƙasa a hannun matasa.
A ƙarshe ta yi kira ga APC ta tsayar da Yahaya Bello kawai ta ga aiki da cikawa.
Discussion about this post