Daga cikin matan da hukumar ta ceto akwai mace daya dake da da namiji mai shekara 3 da kuma mata biyu masu ciki.
Shugaban hukumar NAPTIP Fatima Waziri-Azi ta ce NAPTIP ta yi nasarar ceto wadannan mata a dalilin hada hannun da ta yi da hukumomin NACTAL da A-TIPSOM.
Fatima ta ce hukumar su za ta ci gaba da kokari domin ganin an dawo da sauran mutanen da aka yi safarar su zuwa kasar Mali din daga Najeriya.
“Sakamakon bincike da aka gudanar a shekarar 2017 a kasar Mali ya nuna cewa akwai mutum 20,000 da aka yi safarar su daga Najeriya zuwa Mali.
Bayan haka shugaban kungiya mai zaman kanta NACTAL, Abdulganiyu Abubakar ya ce an samu nasaran dawo da wadannan mata bayan kungiyar ta samu bayanan yadda Matan suka arce daga hannun wadanda suka kama su.
Ya ce hakan ya yiwu ne bayan haɗa hannu da kungiyar ta yi da kungiyoyin kare rajin dan Adam guda 16 a kasashen dake Kudu maso Yammacin Afrika.
Abubakar ya ce a dalilin haka ya sa duka kasashen dake karkashin ECOWAS suka fara amfani da matakan da aka tsara na kare hakkin yara kanana a Afrika.
Ya ce a dalilin haka kasashen dake Afrika ta Yamma suka kafa hukumar WACTISOM da yake taimakawa wajen maida ireiren waɗannan mata da aka yi safara zuwa ƙasashen su.