Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun ta bayyana samun nasarar kama wani mutum da matar sa, waɗanda aka kama da sassan jikin mace sun ɓoye cikin bokitin roba a cikin ɗakin su.
An kama Kehinde Oladimeji ɗan shekaru 43 da matar sa Adejumoke Raji Mai shekaru 35 a gidan su mai lamba 72, kan Titin MKO Abiola, ciki unguwar Leme, a Abeakuta.
Kakakin ‘Yan Sandan Ogun Abimbola Oyeyemi ya ce wani wakilin unguwar ne mai suna Moshood ya kai wa ‘yan sanda rahoton, bayan da wani daga cikin maƙwautan mata da mijin wanda Fasto ne ya ce su na jin wani ɗoyi na fitowa daga ɗakin mata da mijin.
Nan da nan sai DPO na Hedikwatar ‘Yan Sandan Kempa ya tada zaratan sa suka dira gidan.
“An samu sassan jikin mutum da su ka haɗa har da hannaye da nonuwa da ke da alamu cewa na mace ne a cikin bokitin roba a ɗakin su.”
Mijin ya ce shi boka ne, kuma wani mutum ne mai suna Micheal ya kawo masa sassan jikin, domin ya yi masa tsafi da su.
“Jami’an ‘yan sanda sun tasa ƙeyar sa domin ya kai su gidan Micheal ɗin, amma ya yi ta dawurwura da su, ya ce ya kasa gane gidan.
Yanzu dai an maida su a Babban Sashen Binciken Masu Aikata Manyan Laifuka, CIB, domin ci gaba da bincke, kafin a kammala sannan a gurfanar da su kotu.