Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi kwaskwarima a ranakun da ta sanya na manyan zaɓuɓɓukan da za a yi a shekarar 2023, sakamakon rattaba hannu da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kan Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe a ranar Juma’a.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a taron da ya yi da manema labarai kan jadawalin ranakun al’amuran zaɓuɓɓukan na 2023 wanda hukumar ta saki a Abuja a ranar Asabar.
Yakubu ya ce zaɓen shugaban ƙasa da Majalisar Tarayya, waɗanda a da aka sa za a yi a ranar 18 ga Fabrairu, 2023, yanzu an ɗage shi zuwa ranar 25 ga Fabrairu, 2023, yayin da aka ɗage ranar zaɓen gwamnoni da Majalisun Dokoki na jihohi daga 4 ga Maris, 2023 zuwa 8 ga Maris, 2023.
A cewar sa, sakamakon yin wannan gyaran, yanzu sauran kwana 363 cif a gudanar da Babban Zaɓen 2023.
Ya ce, “Shugaba Muhammadu Buhari ya yi abin tarihi da ya sanya hannu a Ƙudirin Zaɓe na 2022 ta hanyar ya kasance karo na huɗu tun daga dawowar mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya a watan Mayu 1999 da aka soke Dokar Zaɓe aka sake ƙirƙiro ta.”
Hakan, a cewar Yakubu, ya ba INEC damar ta fara gabatar da ayyukan manyan zaɓuɓɓukan 2023.
Ya ce, “Za ku tuna cewa a cikin 2017 wannan hukuma ta yanke shawarar ta tsaida ranakun manyan zaɓuɓɓuka a Nijeriya. An yanke wannan shawara ne bisa ƙoƙarin mu na bada tabbaci game da lokutan zaɓen.
“Kuma an yi haka ne domin a bai wa dukkan masu ruwa da tsaki, hukumar zaɓe, jam’iyyun siyasa, da ‘yan takara, hukumomin tsaro, masu sa ido, kafafen yaɗa labarai, da sauran su damar su shirya wa zaɓuɓɓukan sosai.
“Ta dalilin wannan shawarar da aka yanke, an tsara gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da Majalisar Tarayya a ranar Asabar ta uku ta watan Fabrairu ta kowace shekarar zaɓe, yayin da zaɓen gwamnoni da Majalisun Dokoki na jihohi zai biyo baya bayan mako biyu.
“Daga nan, an tsara cewa a fara Babban Zaɓen 2023 a ranar 18 ga Fabrairu, 2023 inda za a yi zaɓen shugaban ƙasa da Majalisar Tarayya, sannan a yi zaɓen gwamnoni da Majalisun Dokoki na jiha a ranar 4 ga Maris, 2023.”
Ya ƙara da cewa: “To amma wannan hukuma ba ta iya sakin cikakken jadawalin da tsarin ayyukan Babban Zaɓen ba, kamar yadda ya kamata a ce ta yi, saboda ana jiran fito da Dokar Zaɓe ta 2022 wadda yanzu an rattaba mata hannu ta zama doka.”
Yakubu ya ce Dokar Zaɓe ta 2022, haɗi da gyararren Kundin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya na 1999, su ne su ka bada damar aiwatar da dukkan zaɓuɓɓuka a Nijeriya.
Ya ce musamman ma dai ita Dokar Zaɓe ta tanadar da tabbatattun lokuta domin aiwatar da ayyukan zaɓe bisa ranar Babban Zaɓe.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin muhimman lokutan da aka tsara shi ne na wallafa Sanarwar Zaɓe wanda bai haura kwanaki 360 ba daga ranar da aka sanya za a gudanar da zaɓe wanda yanzu ya wuce don Babban Zaɓen 2023.
Yakubu ya ce abin da ya biyo baya shi ne hukumar ta yanke shawarar ta gyara ranakun da za a yi Babban Zaɓen 2023 domin tabbatar da an bi ƙa’idojin da doka ta tanadar.
Ya ce a ƙarƙashin dokar, akwai muhimnan ayyukan da lokaci ya ƙayyade daga wallafa Sanarwar Zaɓe zuwa Aiwatar da Zaɓe wanda su ne su ka bada Jadawali da Tsarin Ayyukan zaɓuɓɓukan.
Ya ce: “Wasu daga cikin manyan ayyukan da rabakun aiwatarwar su ne:
“Wallafa Sanarwar Zaɓe – Litinin, 28 ga Fabrairu.
“Gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani, ciki har da warware rigingimu da za su taso daga zaɓuɓɓukan – Litinin, 4 ga Afrilu, zuwa Juma’a, 3 ga Yuni.
“Miƙa fom fom na ‘yan takara ta hanyar gidan yanar INEC don zaɓen shugaban ƙasa da Majalisar Tarayya – ƙarfe 9.00 na safe, a ranar Juma’a, 10 ga Yuni, zuwa ƙarfe 6 na yamma na ranar Juma’a, 17 ga Yuni.”
Shugaban ya ce miƙa fom fom na ‘yan takara ga INEC ta hanyar yanar gizo don zaɓen gwamnoni da Majalisun Dokoki na jihohi zai fara daga ƙarfe 9 na safe a ranar Juma’a, 1 ga Yuli, zuwa ƙarfe 6 na ranar Juma’a, 15 ga Yuli.
Ya ƙara da cewa jam’iyyun siyasa za su fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da Majalisar Tarayya daga ranar Laraba, 28 ga Satumba.
Yakubu ya ce jam’iyyun siyasa za su fara yaƙin neman zaɓe na gwamnoni da Majalisun Dokoki na jihohi daga ranar Laraba, 12 ga Oktoba.
Ya ƙara da cewa ranar ƙarshe da aka ba jam’iyyu su yi yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da Majalisar Tarayya ita ce Laraba, 23 ga Fabrairu, 2023.
Ya ce ranar ƙarshe da aka ba jam’iyyun siyasa su yi yaƙin neman zaɓen gwamnoni da Majalisun Dokoki na jihohi ita ce Alhamis, 9 ga Maris, 2023.
Yakubu ya ce za a ɗora cikakken Jadawali da Tsarin Ayyukan Babban Zaɓen 2023 a gidan yanar INEC da shafukan ta na soshiyal midiya.
Ya ce bugu da ƙari, za a wallafa Sanarwar Zaɓe a ofisoshin INEC da ke dukkan jihohin ƙasar nan, kamar yadda doka ta tanada, a ranar Litinin, 28 ga Fabrairu.
Ya ce da yake yanzu Dokar Zaɓe ta 2022 ta samu, hukumar za ta yi aiki ba ji ba gani domin ta kammala kuma ta wallafa sababbin Dokoki da Jagororin Aiwatar da Zaɓuɓɓuka da su ka yi daidai da Dokar.
Ya ce dukkan waɗannan Dokoki da Jagororin Aiwatar da Zaɓuɓɓuka da kuma Kundayen da hukumar ta fitar wani ɓangare ne na tsarin dokokin zaɓuɓɓukan.
Yakubu ya ƙara da cewa wallafa su da wuri zai bai wa masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓen su saba da tanade-tanaden su a yayin da su ke shirin Babban Zaɓen 2023.
Ya ce: “A nan, ina so in tunatar da masu ruwa da tsaki, musamman jam’iyyun siyasa, haƙƙin da ya rataya a wuyan su na tabbatar da sun yi aiki da lokutan da ke cikin wannan Jadawali da Tsarin Ayyukan, har ma da dukkan sauran tsarin lokutan da hukumar ta bayar.
Ya ce, “Ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa su yi aiki da tsarin dokar da ake da shi, su tabbatar da sun yi tsari mai kyau tare da gudanar da zaɓuɓɓukan fidda gwani da fitar da ‘yan takara da su ka cancanta domin su kauce wa duk wasu shari’u da rigingimu marasa alfanu.”