Kotun Koli ta yi watsi da karar da gwamnonin Najeriya 36 suka shigar wanda suke neman gwamnatin tarayya ta ɗauki nauyi kotun jihohi da kananan kotuna dake jihohin ƙasar nan.
Alkalai hudu ciki bakwai da suka zauna sun amince da haka cewa gwamnonin jihohi ne za su riƙa ɗaukar nauyin kotunan dake jihohin su maimakon kokarin da suke yi na ɗora wa gwamnatin tarayya nauyin haka.
Bayan haka alkalan sun duka sun amince cewa dokar iko da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya saka wa hannu ya saɓa wa dokar ƙasa.
Wannan doka da aka saka wa hannu a shekarar 2020 ya saɓa wa dokar ƙasa.
Dokar da Buhari ya saka wa hannu na tilasta wa jihohi ne su ɗauki nauyin kotunan jihohin su, wanda hakan ya saɓa wa doka.