Majalisar Zartaswa ta amince a kashe naira biliyan 115.4 wajen maida titin da ya tashi daga Kano zuwa Kazaure, Daura har Kwangwalam ya zama mai hannu biyu, irin na Kano zuwa Kaduna.
Wannan titi dai ya tashi daga Kano, ya ratsa cikin Jihar Jigawa ya dangane da Katsina zuwa Kwangwalam, bakin kan iyakar Najeriya da Nijar.
Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola ne ya bayyana wa manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa, wanda aka saba yi kowace Laraba, a Fadar Shugaban Ƙasa.
Fashola ya ce za a ɗauki shekaru biyu ana aikin kafin a kammala shi, kuma za a biya kuɗin aikin ne daga harajin cikin gida da gwamnati ke karɓa.
“Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta gabatar da buƙatar maida titin Kano-Kazaure-Daura-Kwangwalam ya koma titi bai hannu biyu kuma falan-biyu. Tsawon titin kilomita 131.4.
“To Majalisar Zartaswa ta amince a kashe Naira biliyan 115.425.
“Abin alfahari shi ne za a yi wannan aiki daga kuɗaɗen Shirin Aiki Da Kuɗaɗen Haraji na cikin gida. Don haka da kuɗaɗen harajin kamfanin Bua International Limited za a yi aikin. Kuma kamfanin PW Construction Nigeria ne zai yi aikin gina titin.” Inji Fashola.
Shi ma da ya ke na sa jawabi, Ministan Harkokin Sufuri Rotimi Amaechi ya ce an amince a kashe dala miliyan 183.7 wajen biyan ayyukan tuntuɓa wanda masu duba-garin aikin titin jirgin ƙasa guda uku za su yi a nan cikin Najeriya.
Amaechi ya ce ayyukan titinan jiragen ƙasa ɗin sun haɗa da titin Fatakwal zuwa Maiduguri, Kano zuwa Maraɗi da kuma Abuja zuwa Warri.
“Waɗannan ayyukan ginin titina dai daga Kano zuwa Maraɗi, Fatakwal zuwa Maiduguri da Abuja zuwa Warri, har yau ba a fara su ba tukunna.” Inji Amaechi.