Ministan Harkokin Noma da Raya Yankunan Karkara, Mohammed Abubakar, ya jaddada aniya da ƙudirin Gwamnatin Tarayya tabbatar da cewa ta tallafa wa masu kiwon kifi domin a ƙara samun wadatar kifi a ƙasar nan.
Abubakar ya yi wannan alwashin a lokacin da shugabannin Ƙungiyar Masu Kiwon Kifi ta Najeriya (NFAN) ta kai masa ziyara a ofishin sa, ranar Litinin a Abuja.
Da ya ke jawabi, Abubakar ya ce kifi da kuma sana’ar kiwon kifin abu ne mai muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Shi ya sa ya zama tilas ga gwamnatin tarayya ta ga cewa ta tallafi masu kiwon kifi.
“Lallai tabbas kiwon kifi na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin cikin gida. Don haka ina cike da mamaki ganin har yanzu a baya ba ku taɓa cin moriyar komai ba daga gwamnati.” Inji Minista Abubakar.
Yayin da ya ɗauki alƙawarin tallafawa domin Inganta sana’ar kiwon kifi, Abubakar ya ce gwamnati za ta rage farashin kayan abincin kifaye ta hanyar biyan tallafi ta na cike gurbin farashin, domin sauƙaƙe wa manoman kifi.
Minista Abubakar ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ƙarfafa jarin masu kiwon kifi domin kifi ya ƙara wadata.
Ministan Harkokin Noma da Raya Yankunan Karkara, Mohammed Abubakar, ya jaddada aniya da ƙudirin Gwamnatin Tarayya tabbatar da cewa ta tallafa wa masu kiwon kifi domin a ƙara samun wadatar kifi a ƙasar nan.
Abubakar ya yi wannan alwashin a lokacin da shugabannin Ƙungiyar Masu Kiwon Kifi ta Najeriya (NFAN) ta kai masa ziyara a ofishin sa, ranar Litinin a Abuja.
Da ya ke jawabi, Abubakar ya ce kifi da kuma sana’ar kiwon kifin abu ne mai muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Shi ya sa ya zama tilas ga gwamnatin tarayya ta ga cewa ta tallafi masu kiwon kifi.
“Lallai tabbas kiwon kifi na da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arzikin cikin gida. Don haka ina cike da mamaki ganin har yanzu a baya ba ku taɓa cin moriyar komai ba daga gwamnati.” Inji Minista Abubakar.
Yayin da ya ɗauki alƙawarin tallafawa domin Inganta sana’ar kiwon kifi, Abubakar ya ce gwamnati za ta rage farashin kayan abincin kifaye ta hanyar biyan tallafi ta na cike gurbin farashin, domin sauƙaƙe wa manoman kifi.
“Muna da kayan abinci tuli guda. Don haka za mu saka masu kiwon kifi a cikin jerin waɗanda za su amfana da sayen sa ta hanyar farashi mai rahusa. Ku ɗan jira nan da ƙanƙanin lokaci komai zai kankama.”
Dama tun da farko Shugaban Kungiyar NFAN ta masu kiwon kifi, Ladan Aliyu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta tallafi masu kiwon kifi domin su haɓɓaka sana’ar su.
Ya yi ƙorafi tare da nuna damuwa cewa a baya Gwamnatin Tarayya ba ta ja su a jika ba, ballantana ta tallafa masu ta yadda za su bunƙasa wadatar kifi a ƙasar nan.