Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani ingantaccen shiri na shekara 5 wanda Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji, da Inganta Rayuwa za ta yi aiki da shi a tsakanin 2021-2025.
Kundin shirin (Strategic Roadmap) ya na ƙunshe da tsare-tsaren jinƙai da hanyoyin samar da yadda za a yi aiki tare a ayyukan jinƙai na cikin gida da kuma na ƙasar waje.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osibajo, shi ne ya ƙaddamar da shi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja a ranar Litinin.
Mataimakin Shugaban Ƙasar, wanda a taron ya samu wakilcin Mataimakin Shugaban Ma’aikata a fadar shugaban ƙasa, Mista Adeola Rahman Ipaye, ya ce kundin da aka ƙaddamar ɗin wani babban cigaba ne ga Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da ma ita kan ta gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya ce ƙaddamar da ingantaccen kundin wanda ita ma’aikatar ta zauna ta fito da shi ya na da muhimmanci wajen aikin aiwatar da dukkan shirye-shiryen da su ka rataya a wuyan ma’aikatar.
Osinbajo ya ce: “Ina kuma ƙara jin daɗin cewa kundin aiwatarwar ya bada muhimmanci ga alaƙoƙin da ke akwai tsakanin sauran dabarun gwamnati irin su Shirin Cigaban Ƙasa, wato ‘National Development Plan’.
“Da aka sanya shi a cikin faffaɗan tsarin cigaban ƙasa, wannan kundin, da ma ita kan ta ma’aikatar, su na bada gudunmawa ga yanayin bayyanawa tare da tsayawa tsayin daka da kuma rashin yankewa wajen aiwatarwa a dukkan ɓangarorin gudanarwa.
“Haka kuma kundin aiwatarwar ya ƙara tabbatar da muhimmancin aiki tare da juna a tsakanin gwamnatocin tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi, wanda hakan ya na da muhimmanci wajen kawo kyakkyawan sauyi.
“Shi kan shi kundin gudanarwar zai yi tasiri ne idan har an aiwatar da shi yadda ya kamata, don haka a shirye Gwamnatin Tarayya ta ke ta bada tallafi wajen tabbatar da samun nasarar kundin a kowace gaɓa.
“Ina kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa gwiwa su yi aiki tare da ma’aikatar wajen kai mu gaci a ƙudirin mu na samar da ƙasa mai daɗin zama kuma mai lumana.”
Tun da farko a taron, sai da Minista Sadiya Umar Farouq ta bayyana cewa zaunawa a fito da wannan kundin ya zama wajibi ne domin ya samar alƙiblar da za a fuskanta wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyan ma’aikatar.
Ta ce, “Wannan kundi ya kasance sakamako na cikakken nazarin da aka yi kan abubuwan da ke ƙasa da kuma amsoshi da bayanan da aka samu daga sassa da hukumomin da da ke ƙarƙashin ma’aikatar.
“Wannan ingantaccen kundin an yi masa take da ya dace da shi, wato ‘Tsara Rayuwa a Mutunce Don Kowa’ (‘Mapping Out a Life of Dignity for All’), wanda kuma ya yi daidai da babban aikin ma’aikatar na aiwatar da haƙƙoƙi mafi dacewa ga tattalin arzikin ƙasar nan da zaman lafiyar al’ummar ta.
“Haka kuma kundin ya kawo hanyoyin aiwatarwa, sa ido, nazari, dubawa, da bada rahoto waɗanda za a yi amfani da su wajen tabbatar da samun sakamako mai kyau.
“Waɗannan muhimman hanyoyin gane yadda aiki ke gudana da dabarun auna aiki za su ba ma’aikatar damar gane irin nasarar da ta ke samu tare da auna yadda ake aiwatar da kundin tsarin a tsawon shekara biyar, wato daga 2021 zuwa 2025.
“Aiwatar da dabarun da aka tsara sosai da kuma kundin, a yayin da zai haɓaka sassa muhimmai na Gwamnatin Tarayya, zai kuma yi mana jagora wajen cimma nasara a aikin da aka ɗora wa ma’aikatar, da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya marasa galihu, da kuma fito da hanyoyin samar da rayuwa mai daraja ga kowa da kowa.”
Sauran masu jawabi da manyan baƙi a taron ƙaddamar da kundin gudanarwar sun haɗa da Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Alhaji Umar Usman Kadafur, da Ministar Kuɗi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, da Ministan Yaɗa Labarai da Kyautata Al’adu Alhaji Lai Mohammed, da Ƙaramin Ministan Ma’adinai da Ƙarafa, Dakta Uchechukwu Ogah, da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mista Adeniyi Adebayo, da Shugaban Kwamitin Rage Fatara na Majalisar Wakilai, Hon. Abdullahi Balarabe Salame, da Jakaden ƙasar Dubai a Nijeriya, Dakta Fahad Obaid Al Taffaq, da Babban Sakatare na ma’aikatar da ta shirya taron, Alhaji Bashir Nura Alƙali, da shugabannin hukumomi da daraktocin ma’aikatu da na ƙungiyoyi masu zaman kan su da kuma wakilan shugabannin hukumomin tsaro, naƙasassu, al’umma da hukumomin bada agaji da ake aiki tare da su.