Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin 2023 wadda za ta gaje shi, za ta gaji tattalin arzikin ƙasar da aka bunƙasa ta hanyar inganta harkokin noma a cikin ƙasa, ingantacciyar dimokraɗiyya da ƙarfafan hukumomin tsaron da aka farfaɗo da su.
Buhari ya yi wannan jawabi ne a wurin taron shekarar 2022 domin karrama Kwamitin Shugabannin Harkokin Kasuwanci, Siyasa, Kafafen Sadarwa da Kungiyoyin Kare Haƙƙi, Buhari ya ce ya na fata da kuma ƙoƙarin ganin ya bar kyakkyawan tarihin barin Najeriya a cikin halin bunƙasa da ci gaba da haɗin kai da zaman lafiya, tsawon shekaru 24 ba tare da an yi wa dimokraɗiyya karan-tsaye ba.
Buhari ya ce gwamnatin sa za ta kammala wa’adin ta a cikin karsashi na nagartar ta a shekarar karshen mulkin sa.
” Yanzu dai ina kan hanyar shiga shekara ta ƙarshen mulki na. Lokaci ne da na ke so na ga na ƙara kafa wa nasarorin da na samu ginshiƙai a tsawon shekaru bakwai da na yanzu. Kuma na ga ba bar Najeriya a matsayin dunƙulalliyar ƙasa mai zaman lafiya da albarka.
“‘Yan siyasar cikin ku su daina haƙilon hawa mulki ki muƙami kawai, su riƙa tunanin yadda za su yi amfani da muƙamin domin su kawo canji a cikin al’umma.
“Haka manyan ‘yan kasuwar ku maza da mata, su sani cewa akwai martaba sosai a cikin aikin gwamnati da yi wa ƙasa ayyukan inganta ƙasa.
“Babbar abin tambaya ita ce shin ta yaya za mu yi amfani da albarkatun kasuwancin mu mu bunƙasa ƙasar mu?”
“Idan za a lura na sha sukar manyan mu da manyan ‘yan bokon mu, saboda wasun mu sun sha nuna cewa ba mu iya jurewa mu daina nuna ra’ayin son rai, bambancin siyasa da ƙabilanci da addinnanci a lokacin da buƙatar haɗin kai don ci gaban ƙasar mu ya taso.”
“Sannan kuma a cikin shugabannin mu da manyan mu akwai waɗanda su dai su ci riba kaɗai su ka sani, ita ce babbar buƙatar su a kowace harka.”
Buhari ya gode wa kwamitin saboda irin yadda ya kauda kai daga ririta ƙabilanci da addinanci.
Yayin da Gwamna Kayode Fayemi ke magana, gwamnan na Ekiti ya nuna damuwar sa kan afkuwar juyin mulki a wasu ƙasashen Afrika, Buhari ya ce to shi dai alfaharin da ya ke yi, shi ne a yanzu dai Najeriya ta wuce wannan batun, juyin mulki ya zama tarihi a Najeriya.