Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta gano wani gurɓataccen man fetur wanda aka garwaya da man Methanol da shi, kuma aka shigo da shi cikin ƙasar nan.
Wannan gurɓataccen mai ne a cewar gwamnati ya haddasa ƙarancin fetur, wanda ya haifar da dogayen layukan shan mai a Legas da Abuja da wasu muhimman biranen ƙasar nan.
Gwamnati ta ce samfurin ‘methanol’ dama ba abu ba ne bambarakwai, saboda a kan same shi a cikin fetur, shi ya sa aka ware dukkan sauran fetur ɗin da ya garwaya da ‘methanol’ daga gidajen mai.
Haka dai Hukumar Kula da Tsarin Ƙayyade Fetur ta NMDPRA ta bayyana a ranar Talata, a Abuja.
Kusan shekara ɗaya kenan mazauna Abuja da Legas na gaganiya da matsalar fetur, inda gidajen mai ke sayarwa yadda su ka ga dama, maimakon yadda ake buƙata.
A kullum ita kuma gwamnati sai iƙirari ta ke yi cewa ta na da wadataccen mai ajiye, yadda ba zai yanke ba.
Wannan sabuwar matsalar ƙarancin fetur kuwa ta samo asali ne tun cikin 2021, lokacin da gwamnati ta bijiro da shirin ƙarin kuɗin fetur, wanda daga nan aka riƙa zargin manyan dillalan fetur da ɓoye shi. Sannan kuma ake cewa duk da gwamnati ta janye lissafin janye tallafin, su manyan dillalan fetur ɗin ba su fito da shi ya wadata ba har yanzu.
A Abuja babban birnin Tarayya kusan kwana 20 ana fama da matsalar fetur. A ranar Talata wakilin mu ya zagaya gidajen mai da dama. Wasu na rufe, su kuma waɗanda ake sayar da mai, akwai cincirindon motocin haya, na masu zaman kan su da kuma ‘yan-gada-gada.
Wata matsalar da ƙarancin man ke haifarwa ita ce rashin bin doka da ƙa’idar tuƙi. Yayin da na kan layin sayen fetur ke cika kan titina, hakan na sa masu wucewa a guje na komawa su na bin hannun masu tahowa.
Yayin da waɗanda suka rigaya su ka sha wancan fetur ke korafi, zage-zage har da Allah ya isa, da dama na cewa, ruwa aka antaya wa fetur ɗin.
Wasu kuwa na ganin cewa babu yadda za a yi a ce ba a san da matsalar ba tun da farko, “domin fetur ɗin da ya gurɓacen ya yi kama da kunun kanwa ko kunun jego.”
“Mu kuma an bar mu da asarar sayen gurɓataccen fetur da kuma asarar biyan kuɗin gyaran motocin mu da gurɓataccen fetur ya haifar mana.”