Idan aka ajiye batun adawa, ko siyasar ɓangaranci da ƙabilanci a gefe, to za a iya cewa Sanata Abubakar Bukola Saraki (ABS) ya dace da shugabancin Najeriya a 2023. Domin idan za a yi zube-ban-ƙwaryar dukkan waɗanda suka nuna sha’awa ko kwaɗayin fitowa takara, babu wanda ya isa ya ture Saraki daga sahun gaba.
A mulki da siyasa dai an fi sanin Saraki gadan-gadan daga lokacin da ya zama Gwamnan Jihar Kwara tsakanin 2003 zuwa 2011.
Bayan kammala wa’adin sa, Saraki ya yi takarar zaɓen fidda gwanin neman fitowa zaɓen shugaban ƙasa a 2011. Sai dai duk da bai samu tikiti ba, ya samu nasarar zama sanata daga Jihar Kwara.
Da guguwar 2015 ta kaɗa, Saraki na a sahun gaban dakka da gaggan waɗanda su ka fice daga PDP, suka koma APC, har ta kai ga Buhari ya yi nasara.
Saraki ya sake nasara kan kujerar sa ta sanata a ƙarƙashin APC. Sai dai a lokacin ne gogan ya nuna wa duniya cewa idan ma ana gadon siyasa, to ya da gaje ta ɗin. Mahaifin sa Olusola Saraki ya yi Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, a zamanin Jamhuriya ta Biyu, wadda aka fi sani da zamanin mulkin Shagari.
Lokacin da aka yi gambizar da ta yi sanadiyyar nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a 2015, an ƙulla yarjejeniyar bai wa nPDP muƙamin Shugaban Majalisar Dattawa, kamar yadda aka bai wa ACN muƙamin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Sai dai kuma bayan APC ta yi nasara, an samu akasi a ɓangaren shugaban ƙasa da ‘yan barandan sa, waɗanda suka nemi yi wa Saraki buƙulun zama shugaban majalisar dattawa.
Amma da ya ke Saraki ya san kan-tsiyar siyasa, sai ya nuna shi ai tamkar kurege ne, uban dabarar da ba ya yin rami ƙofa ɗaya.
Fadar Shugaban Ƙasa ba ta ankara ba sai dai ji kawai suka yi har an naɗa Saraki ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Daga lokacin sai aka riƙa yi faɗan zalɓe da maciji tsakanin Fadar Shugaban Ƙasa da Sanata Saraki.
Zalɓe ne ya haɗiyi maciji dai kan sa. Shi kuma maciji ya kanannaɗe wuyan zalɓe, ta yadda ya kasa haɗiyar miyau ballantana ma ya iya haɗiyar macijin.
Bukola Sarakin Shugaban Majalisar Da Bai San Amshin-Shata Ba:
Shekaru huɗu da Saraki ya yi a shugabancin Majalisar Tarayya, ya ji jiki, amma kuma shi ma ya jigata Fadar Shugaban Ƙasa. Domin a Tarihi ba a taɓa yin Shugaban Majalisar da ya tsone wa Shugaban Ƙasa ido kamar sa ba.
Babu irin tuggu, ‘jamhuru’, kitimirmira da kutunguilar da ba a kitsa wa Saraki ba, don dai a ga bayan sa. Amma ba a yi nasara ba.
Sai da ta kai tun ana bin sa da ƙullin maka shi kotu ya na Shuagaban Majalisar Dattawa, har sai da ta kai ana yi masa barazana da jami’an tsaro. Amma dakakken ya dake, ko gezau.
An kewaye gidan sa, an hana shi fita. An janye masa jami’an tsaro. Kai an, an, an ɗin da aka yi masa su na da yawa. Da mai rarraunar zuciya, da Saraki ya kwanta ƙasa ya yi liƙis, sun bi shi sun ƙarasa.
An bi Saraki da sharri a lokacin, ta yadda duk matsalar da ta faru sai a ce don Saraki na Shuagaban Majalisar Dattawa ne. Sai ga shi bayan ba ya kan kujerar ne ma matsalolin suka fi dabaibaye Najeriya.
Bajekolin Saraki A Zahiri Da Baɗini:
Da dama ba su san baɗinin Saraki ba a lokacin da ya na Gwamnan Jihar Kwara daga 2003 zuwa 2011. Zahirin sa aka fi sani a Majalisar Dattawa.
Bukola Saraki ba ɗan siyasar da za a yi wa gorin rashin iya rigimar siyasa ba ne. Da kowa ma zai iya. Shugaban Muhammadu Buhari da kuma ‘yar’uwar Sarakin Gbemisola Saraki za su iya tabbatar da haka.
Idan batun zaman lumanar siyasa ce, nan ma a sahun gaba ya ke, domin shi ne ma Shugaban Kwamitin Sasanta Hasalallun PDP.
Idan ka ɗaga Saraki a kasuwar hada-hadar darajar ‘yan siyasa, da wahala ka samu wanda zai fi shi farashi ko nauyi.
Tsawon shekaru takwas ɗin da ya yi ya na gwamna a Jihar Kwara, sun isa shaida cewa idan ya samu damar riƙe Najeriya, ba zai yi wasarere da akalar mulki har a koma ana da-na-sanin shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yin yaya-za-a-yi ba.
Kaɗan daga abin da al’ummar Jihar Kwara ba za su manta da Saraki ba, shi ne ƙoƙarin sa wajen:
Haɗa garuruwa 375 da tashar wutar lantarki ta ƙasa.
Samar da taransafoma har 735 ga al’ummar garuruwa da yankunan karkara.
Warkar da mutum 45,526 daga cututtukan da suka haddasa masu gani garara-garara ko dundimi.
Yi wa mutum 2,630 aikin warkar da makanta, su ka koma gani Tangaran.
Inganta ilmin firamare da sakandare, ta hanyar samar da wadatar ƙwararrun malamai. Kafin saukar Saraki ta kai yawan malamai za su kai duk ɗalibi ƙasa da 20 na da malami 1. Ba kamar wasu jihohi ba da za ka samu malami 1 da ɗalibai 70 ko fiye da haka.
Saraki ya gina Jami’ar Jihar Kwara a cikin 2009.
Ya inganta matasa ta hanyar gina Cibiyar Bunƙasa Wasan Kwallon Ƙafa ta farko a Najeriya (Kwara Football Academy).
Ya bunƙasa harkokin noma, musamman kafa Shonga Farm, wadda yanzu haka a fannin kiwon kaji ta na cikin manyan gonakin da ake tinƙaho da su a ƙasar nan.
Saraki ya inganta samar da ruwa a dukkan mazaɓu 193 na Jihar Kwara. Ya jina famfon burtsa 1,930 a cikin shekara ɗaya (2006-2007). Wato kowace mazaɓa famfo 10 kenan.
Saraki ya gina rukunin gidaje masu sauƙin kuɗi a wurare 9.
Zamanin mulkin Saraki ne ya gina sabbin Ofisoshin ‘Yan Sanda har guda 25 a cikin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Ya bunƙasa hanyoyin samun kuɗin shiga a jihar, daga naira miliyan 64 a duk wata zuwa naira milyan 300 duk wata.
Lokacin da Saraki ya hau mulki cikin 2003, ya gaji bashin naira biliyan 42, amma kafin ya sauka sai da ya biya bashin kakaf.
Ya bayar da bashi har na naira biliyan biyar ga ma’aikatan gwamnati da sauran masu riƙe da muƙamai a Jihar Kwara, domin su sayi hannayen jari a kasuwar hada-hadar hannayen jari.