Hankulan wasu gaggan jami’an hukumomin gwamnati da wasu manyan ma’aikatan bankuna ya tashi, yayin da Hukumar EFCC ta fara binciken zargin yadda Hukumar Ƙwace Kadarorin Masu Taurin Bashi (AMCON), ta sayar da kadarorin naira biliyan 114, waɗanda ta ƙwace daga hannun wasu gurzagullan ɓarayin ɗanyen mai, Akanni Aluko da Jide Omokore.
EFCC ta gayyaci Shugaban AMCON Ahmed Kuru, amma dai har yanzu babu takamaiman irin zafafan tambayoyin da aka yi mana tukunna, ba su fito fili ba.
Daga nan kuma PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa EFCC ta faɗaɗa binciken ta har zuwa kan wasu ‘Yan Majalisar Tarayya, jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN), jami’an First Bank da na Polaris Bank waɗanda duk ake zargin sun shiga sun fita wajen yin dillanci ko daƙa-daƙa da gadangarƙamar sayar da kadarorin.
Aluko Da Omokore: Manyan ‘Yan Gudubalen Ɗanyen Mai:
Aluko da Omokore sun tsere daga Najeriya bayan da kamfanin su mai suna Atlantic Energy ya afka cikin kwatamin badaƙalar dala biliyan 1, ruwan da ya ci tsohuwar Ministar Fetur, Diezani Allison-Madueke.
AMCON ta gaji bashin da First Bank da Polaris Bank ke bin su, kuma ta ƙwace kadarorin su, domin ta sayar ta biya First Bank da Polaris Bank bashin da su ke bin su.
Shugabanni Ko Tantiran Ɓarayi:
Wata ƙwaƙƙwarar majiya a cikin EFCC ta gulmata wa PREMIUM TIMES cewa AMCON ta kaɗas da kadarorin kan Naira Biliyan 114 ga wasu ‘Yan Majalisar Najeriya da kuma wasu manyan Jami’an Babban Bankin Najeriya (CBN) da manyan jami’an First Bank da na Polaris Bank.
Sannan kuma maimakon AMCON ta ajiye kuɗaɗen Asusun Gwamnantin Tarayya, sai ta kimshe su a First Bank da Polaris Bank.
Mugu Shi Ya San Makwantar Mugu: Yadda Aluko Da Omokore Suka Dawo Da Kadarorin Su A Asirce:
Premium Times ta ji cewa Aluko da Omokore sun kewaya wurin waɗanda su ka sayi kadarorin su a ɓagas daga hannun AMCON, su ma suka sake saye a hannun su a ɓagas.
Yadda EFCC Ta Bada Belin Kuru Kan Naira Biliyan 114:
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa EFCC ba ta saki Ahmed Kuru ba, har sai da First Bank da Polaris Bank suka damƙa wa hukumar rubutaccen alƙawarin sharaɗin biyan Naira Biliyan 114 tukunna, kwatankwacin adadin kuɗin da AMCON ƙarƙashin Kuru ta kaɗas da kadarorin.
Kakakin First Bank da na Polaris Bank sun ƙi amsa tambayoyin PREMIUM TIMES.
Shi kuma Kakakin AMCON cewa ya yi, “gayyatar Ahmed Kuru kaɗai aka yi zuwa EFCC, ba tsare shi aka yi ba.”
Ana ci gaba da bincike.