Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya ragargaji jagoran APC Bola Tinubu, ya ce ya dasa masu Gwamna “mugun iri” a Jihar Osun.
Da ya ke wa dandazon magoya bayan APC jawabi cikin harshen Yarabanci a garin Ijebu-jesa, Aregbesola wanda shi ya yi gwamna tsawon shekaru takwas sannan ya sauka Gwamna Gboyega Oyetola ya gaje shi, ya ce ya amince da Oyetola ya zama gwamna ne bayan Tinubu ya bada shi a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi, kuma ya yi alƙawarin zai ɗora kan ayyukan raya ƙasa da Aregbesola ya kafa a Osun.
“Amma Oyetola na hawa a 2018 kujerar gwamna, sai ya kauce, ya saki hanya, ya shiga daji kuma ya karya alƙawari.”
Daga nan sai Aregbesola ya ce “kamar yadda Tinubu da mutanen sa su ka yi wa tsohon Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode saboda ya saki hanya, su ma a Jihar Osun haka za su yi wa Oyetola tunda ya saki hanya.”
“Kamar yadda aka yi a Legas, mu ma a Osun za mu yi amfani da ƙuri’u mu watsar da mugun irin da aka dasa mana, maras cika alƙawari.” Inji Aregbesola.
“Ku je ku shaida masu mu ke da jam’iyyar nan. Kuma mu ne ‘yan Afenifere na gidi. Mu ke ƙyanƙyasar Awolowo da Bola Ige.
“Wannan jam’iyya APC ta mu ce, mu ba ‘ya’yan bora ba ne.”
Can da jawabi ya yi zafi, Aregbesola ya fito ƙuru-ƙuru ya na ragargazar Tinubu da Gwamna Oyetola, har ya na yi masu waƙa da Yarabanci, ya na cewa, “adabo da gayyar tsiya.”
“Yanzu mun dawo gida domin mu ɗora jam’iyyar mu a kan hanya, ta yi saitin tafiya sosai a kan miƙaƙƙar hanya.
“Mun bi mutumin nan, mun yi tsammani nagari ne. Wasu ma har ƙoƙarin fitar da mu daga Musulunci su ka yi don mun bi shi. Mun riƙe shi amana babu sharri, amma ba mu sani ba ashe shi sharri ya ke ƙulla mana.
“Mun kai shi inda Ubangiji bai kai shi ba. Shi kuma ya riƙa ɗaukar kan sa kamar wani ubangijin bautar mu.
“Mu kuma mun rantse sai mun tozarta duk wani da ya ɗauki kan sa tamkar ubangiji.
“Mu muka gina wannan jam’iyya bayan mun sha wahala da gumi har wasu da dama mun rasa su. Mun hau mulki ranar 27 Ga Nuwamba, 2010. Mun yi mulki shekaru takwas, a bisa adalci kamar yadda Allah ya ce mu yi adalci. Kuma jama’ar Osun sun ji daɗin mulkin mu.”