A ranar Litinin ne Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe ya sanar da manema labarai cewa an ɗage Taron Gangamin APC na Ƙasa da aka shirya yi a ranar Asabar, 26 Ga Fabrairu, 2022.
Ya ce Kwamitin Tsarawa da Shirya Taron na Ƙasa ya ce za a yi shi yanzu a ranar 26 Ga Maris, a Abuja.
Ya shaida wa manema labarai haka, bayan Kwamitin Shirya Taro ya yi ganawar sirri inda suka nuna wajibcin ɗage taron.
Akpanudoedehe ya sanar da ‘yan jarida cewa APC ta sanar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) sabuwar ranar da aka aza ta 26 Ga Maris.
Ya ce ya sanar da INEC cewa a cikin lokacin ne za a yi taron gangami na shiyyoyin ƙasar nan, kafin ranar gangami na ƙasa baki ɗaya da za a gudanar a ranar 26 Ga Maris.
Ɗage taron dai na da nasaba da kimshin rikice-rikicen da APC ke ciki, tun daga kan cikin uwar jam’iyya ta ƙasa, har zuwa cikin shugabannin jihohi da na ƙananan hukumomi masu yawan gaske a ƙasar nan.
Makonni biyu PREMIUM TIMES Hausa ta yi nazarin waɗannan rikice-rikicen. Ga su nan dalla-dalla, a karanta domin sauƙin gane yadda rikicin ya kunno.
Gangamin APC: Salsalar Rikicin Da Ya Hana Tulin Tsintsiyar Najeriya Share Filin Taron Abuja:
Sarƙa Uwar Rikici: Yadda Rigingimu Suka Yi Wa APC Tarnaƙi da dabaibayin Wahalar Tsallake Siraɗin 2023:
Masu nazarin siyasa da masu jefa ƙuri’a baki ɗaya, sun yi tunanin jam’iyyar APC za ta kame kan ta daga irin zubar da kima da mutuncin da PDP ta yi, har ta rasa mulki bayan shafe shekaru 16 a jere.
Rigingimu su keta PDP cikin 2006 da kuma 2014, waɗanda su ka ja mata asarar mulki, lamarin da har yau APC ba ta daina yi mata bi-ta-da-ƙulli ba, tun bayan faɗuwa zaɓe cikin 2015.
Shekaru bakwai ɗin da PDP ta yi zuwa yau ta kasa kimtsa kan ta. Daga yau ta yi wawan-zama a tsakiyar kasuwa kowa na kallon al’aurar ta, gobe kuma sai ta ɗibga tulin abin kunya, ta yi sata gidan surukan ta. Ki kuma ka ga dangin uwar APC sun kaure faɗa tsakanin su da dangin uba.
APC wadda auren gamin-gambizar ACN, CPC, ANPP da APGA ne suka haife ta, shugaban ta na farko shi ne Bisi Akande.
Tun a ranar 6 Ga Fabrairu, 2013 aka fara batun yin gambiza, amma sai bayan wata biyar aka yi mata rajista, a ranar 31 Ga Yuli, ,2013. Daga nan ta yi mulki a 2015 , sannan ta sake lashe zaɓe a 2019.
Shekaru 9 bayan kafa APC, wannan jam’iyya mai mulkin ƙasa mai yawan al’umma miliyan 200, ta shiga rikici, ta afka cikin gararin da ke neman gagarar ta sasantawa.
Tun bayan sauke Adams Oshiomhole daga shugabanci APC ba ta sake zama lafiya ba. Dama kuma cutar amai da gudawar da jam’iyyar ta yi fama da shi ne a ƙarƙashin shugabancin Oshiomhole ya sa aka cire shi.
An naɗa Shugabannin Kwamitin Riƙo na Mutum 13, a ranar 25 Ga Yuni, ƙarƙashin Gwamna Mala Buni na Jihar Yobe. Aka ɗora masa alhakin shirya taron gangami ƙasa, cikin watanni shida. Amma har yanzu fiye da shekara ɗaya kenan, Buni ya kasa gudanar da taron gangami.
Hakan ya sa gwamnonin APC yin taro a cikin Nuwamba, 2021 a Abuja suka aza rana cewa za a yi gangami a cikin Fabrairu, 2022.