Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayar da kwangilar tantance kadarorin gwamnatin tarayya na biliyoyin nairori ga wani kamfani da lauyoyi a asirce.
Kamfanin da ya taki sa’ar wannan gadangarƙamar dai sunan sa Gerry Ikputu & Partners, wanda kuma kamfanin tantance darajar farashin maka-makan rukunin gidaje ne, wanda shi ma ya tattago wani kamfanin lauyoyi mai suna M. E. Sheriff & Co, a matsayin ejan ɗin kwangilar.
Kashe Mu Raba Ba Sata Ba, Almundahana Ce:
Minista Malami ya umarci kamfanin ya binciko yawan filaye, gonaki da maka-makan gine-ginen Gwamnatin Tarayya a waɗansu jihohi 10 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
2. Za su ɗauki kashi 3 bisa 100 na ilahirin kadarorin da su ka gano.”
Haka dai yarjejeniyar kwangilar ta ƙunsa, wacce aka yi a asirce, kuma mai ƙunshe da ƙa’idojin sirri cewa kada su kuskura su bayyana wa jama’a kwangilar.
3. Sharuɗɗan da aka rattaba sun ce kada ‘yan kwangilar su bayyana wa bainar jama’a aikin kwangilar, ba tare da umarnin Ministan Shari’a Abubakar Malami ba.”
4. Amma kuma an gano cewa Sashen Bincikowa da Tantance Kadarorin Gwamnatin Tarayya na Ma’aikatar Shari’a wanda aka umarta su yi aikin tare da kamfanonin, ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka rattaba ɗin duk bige ce kawai da bagaraswa, ba sahihiya ba ce.
Malami ya bayar da kwangilar ga M. E. SHeriff & Co cewa ya gano tare da tantance kadarorin a cikin watanni shida.
Adadin kwanakin watannin da Malami ya bai wa kamfanin dai zai ƙare a cikin watan Afrilu. Haka dai yarjejeniyar kwangilar da aka rattaba a ranar 5 Ga Oktoba, 2021 ta nuna.
Malami ya umarci kamfanonin su riƙa kai masa rahotannin yawan adadin abin da suka gano a duk wata.
Irin Kadarorin Da Aka Kafa Wa Kahon-zuƙa:
Wasiƙar yarjejeniyar ta faɗo hannun PREMIUM TIMES. An rubuta ta a ranar 5 Ga Oktoba, 2021, ta ƙunshi shi jerin sunayen kadarorin da za a tantance a jihohi 10 da Abuja.
Kadarori 74 ne ake so a binciko tare da tantance su a Legas, Ribas, Akwa Ibom, Cross Riba, Abia, Anambra, Edo, Enugu, Imo da Delta.
PREMIUM TIMES Hausa na da jerin sunayen kadarorin da ake so a gano har 74, waɗanda daga ji da gani za a san cewa kamfanonin ba wani jan aiki ne za su yi ba, domin kowane gini ko fili akwai adireshin wurin da ya ke.
Haka kuma ganin sunayen sauraren zai sa mai karatu ya gane cewa kamfanonin za su kuɗance idan aka ba su kashi 3 bisa 100 na yawan kadarorin.
Yarjejeniyar dai ta nuna ba za a biya su kashi 3 ɗin ba, har sai bayan sun kammala aikin na su.
Babban Lauya Itse Sagay ya ce wannan kwangila haramtacciya ce, domin bai kamata a bai wa wani kamfani aikin ganowa da tantance kadarorin gwamnatin tarayya ba, alhali ga hukumomin Gwamnantin Tarayya irin su EFCC da ICPC, waɗanda su ne ya dace a bisa tsarin doka su yi aikin.