Gwanin siyasa kamar gwanin rawa ne, domin da rawa da siyasa duk yadda ka kai ga iya su, wata rana sai sun kayar da kai.
Bisa dukkan alamu hakan na neman faruwa ga jagoran APC.
Bola Tinubu, a ƙoƙarin da ya ke yi na ganin ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, kuma ya yi nasara a 2023.
Saboda tsananin iya kokawar siyasar Tinubu, tun ya na gwamna ya kafsa da shugaban ƙasa na lokacin, Olusegun Obasanjo, kuma ya yi nasara a kan sa. Sai da ta kai dukkan gwamnonin da su ka ja da Obasanjo na yankin Yarabawa ba su yi tazarce ba a 2003. Amma Tinubu sai da ya zarce.
Sannan kuma kowa ya san rawar da ya taka wajen ganin yankin Kudu maso Yamma ya karɓi Shugaba na yanzu da kuma APC a 2015 da kuma 2019.
Sai dai kuma yayin da ya rasa kujerar takarar mataimakin shugaban ƙasa a 2015, ya haƙura ya bar wa yaron sa Yemi Osinbajo, a yanzu ma ƙoƙarin da Tinubu ke yi na ganin ya zama shugaban ƙasa, ya fara cin karo da cikas tun a cikin yankin sa na Kudu maso Yamma.
Kwanan baya PREMIUM TIMES Hausa ta yi sharhi a kan yiwuwar nasara ko alamomin rashin nasara ga Tinubu a takarar 2023.
Sannan kuma jaridar ta buga labarin yadda Babban Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ojudu ya fito ya kware wa Tinubu baya cewa shi fa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo zai bi a takarar 2023, ba zai bi Tinubu 2023 ba.
A makon jiya shi ma Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, wanda yaron Tinubu ne, har ma Kwamishina ya yi a Jihar Legas, a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ya fito ya ragargaji jagoran su Tinubu.
Jerin Carbin Wasu Da Ke Sacce Tayoyin Tirelar TINUBU 2023 A Dokar Daji:
Yayin da sai a cikin watan Yuni za a fara miƙa wa Hukumar Zaɓe sunayen ‘yan takara, tuni wasu manya da ƙanana a ƙasar nan sun fara sacce wa Bola Tinubu Tayoyin Tafiyar 2023:
Obasanjo Da IBB: Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo shi da Tsohon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida, duk sun shawarci Tinubu ya haƙura, ya zauna ya ririta kula da tsufan sa, ya bar Yemi Osinbajo ya fito takara.
Dattijon Neja-Delta Edwin Clerk: Tsohon Minista na tun ‘tele-tele’, Edwin Clerk, Wanda ubangidan Tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ne, ya ce ba zai taɓa zaɓen Tinubu ba, shi dai Osinbajo zai zaɓa, kuma shi zai ce a zaɓ. Clerk kowa ya sani mutum ne mai faɗa-a-ji a Neja-Delta.
Tawagar Rataya ‘Yan 13×13: Wannan tawaga ce ta mawaƙa da ‘yan fim da su ka dulmiya tsundun a cikin siyasar neman biyan buƙatar kai. Rarara wanda ya yayata Buhari a 2015 da 2019, shi da tawagar sa sun yi wa Osinbajo kyakkyawar tarba a Kano. An riƙa watsa wani bidiyon su da su ka ɗauki hoto a tsaye, kuma a tsayen su na yi wa Mataimakin Shugaban Ƙasa ɗin waƙa sauran dandazon ‘yan fim na amsawa: “Osinbajo na Baba Buhari.”
Kalaman da su Rarara, Baban Chinedu da sauran su ke rerawa, sun nuna lallai akalar siyasar aƙida ko ta rashin aƙidar ‘yan fim ɗin ta karkata wajen Osinbajo, ba wajen Tinubu ba.
Ƙoƙarin Taka Wa Jibrin Kofa, Kofaton Dokin Tinubu Burki:
Cikin makon jiya PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa an aika wa Abdulmumin Jibrin sammacin gayyata a Ma’aikatar Ayyuka Da Gidaje. Duk da dai ba san dalilin ba, masu sharhi na cewa gayyatar ba ta rasa nasaba da kunnen da za a ja masa, saboda ya shiga rigimar tallar Tinubu alhalin ya na ma’aikacin gwamnatin tarayya.
Kofa dai shi ne Shugaban Hukumar Gidajen Gwamnatin Tarayya (FHA). A dokance ya karya dokar aikin gwamnati a Najeriya.
Bibiyar Tirka-tirkar TINUBU 2023:
“Na Fi Ƙarfin Wasu ‘Yan Iska Su Tilasta Ni Bin TINUBU 2023’ -Ojudu Mashawarcin Buhari:
Yayin da aka fara kaɗa gangar zaɓen 2023, kuma har wasu jiga-jigai sun fara karkarwa su na kirari, ɗaya daga cikin wanda ya nuna maitar neman tsayawa takara a ƙarƙashin APC, shi ne jagoran jam’iyyar Bola Tinubu.
To sai dai tun tafiya ba ta ma kai ga batun fitowa yankan tikitin takara ba, Tinubu ya fara haɗuwa da cikas.
Wasu da aka riƙa danganta su da Tinubu sun riƙa fitowa su na ƙaryatawa, musamman Ƙungiyar Yarabawa Zalla (OPC), Dele Mamudu da wasu daban.
A jiya kuma Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a kan Al’amurran Siyasa, Babafemi Ojudu, ya fito ya bayyana cewa ba zai goyi bayan kamfen ɗin ubangidan sa Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa ba.
Ojudu wanda yaron Bola Tinubu ne a baya, ya ce amma fa kada jama’a su ka matsayar da ya ɗauka a matsayin cin amana.
Cikin Wata sanarwar da ya fitar a shafin sa na Facebook a ranar Talata, Ojudu wanda ya ce shi da Tinubu sun daɗe su na tafiya tare, “to amma a gaskiya mutunci na da tunanin da zuciya ta ke nuna min, ba daidai ba ne na goyi bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa.”
Ojudu da Tinubu sun fara shaƙuwar siyasa tun farkon 1990, inda tsohon gwamnan Lagos ɗin da kuma ɗan jarida Ojudu, wanda ya koma ɗan siyasa ya zama sanata.
Tinubu ya narka kuɗi a mujallar TheNews, wadda mallakin Ojudu da wasu abokan sa ce a lokacin.
Sai dai kuma a cikin 2016, Buhari ya naɗa Ojudu Mashawarcin Shuagab Ƙasa a Harkokin Siyasa, kuma ya umarce shi da ya yi aiki tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Duk da cewa Tinubu ne tsanin da aka taka aka ɗora Osinbajo kan kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa, tun tafiyar ba ta yi nisa ba su ka raba hanya, babu jituwa a tsakanin su.
Ana ganin dai a yanzu Ojudu ya ɗauki hanyar goyon bayan takarar Osinbajo, kuma ya fara tallar sa a zahiri da baɗini.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, tsohon sanatan ya ce har an fara yi masa barazana, kuma iyalin sa ma ana yi masu bsrazana, saboda kawai matsayar da ya ɗauka ta ƙin mara wa Tinubu baya.
“Kada ma wani ya yi tunanin cewa zai iya tirsasa ni yin abin ca mutunci na da zuciya ta ba su amince min na yi ba.” Inji Ojudu.
“Masu yawan kiran waya ta su na yi min barazanar banza da wofi da masu neman su kunyata iyali na, su daina haka nan.
“Na san Tinubu. Ina girmama shi. Da yawan waɗanda ke goyon bayan sa a yanzu, ba su ma san wane ne Tinubu ba. Da sun san wane ne Tinubu da ba su tsaya su na tayar da jijiyar wuya a kan sa, har su na neman ci min mutunci ko kai min hari ba.
“Lokacin da Tinubu ya ƙi goyon bayan takarar Obasanjo a 2003, ba a kira shi maci amanar jinsin Yarabawa ba ko maci amanar Afenifere.
“Ya zaɓi abin da ran sa ya biya masa a lokacin, kuma tarihi ya yi masa hukunci da alƙalanci. To ni ma ina so tarihi ya yi min hukunci da alƙalanci.
“Kuma lokacin da Tinubu ya goyi bayan Olu Falae maimakon jagoran mu Bola Ige, ai babu wanda ya kira shi Tinubu ɗin maci amana.
“Ku kuma ƙananan ‘yan iskan da ke ta aiko min da saƙonnin waya ku na yi min barazana, ni da iyali na, kuma ku na surfa min zagi don na ƙi goyon bayan Tinubu, ku sani hakan ba dimokraɗiyya ba ce.
“Na shafe shekarun tasowa ta a rayuwa ina yaƙi da danniya da masu danniya da masu mulkin soja. To har yanzu a shirye na ke, kuma ba zan saki abin da zuciya ta ta fi kwantawa da shi ba, ko da kuwa za a ɗauki rai na.”
Yadda Minista Aregbesola Ya Gurgunta Dokin Sukuwar TINUBU 2023:
Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola ya ragargaji jagoran APC Bola Tinubu, ya ce ya dasa masu Gwamna “mugun iri” a Jihar Osun.
Da ya ke wa dandazon magoya bayan APC jawabi cikin harshen Yarabanci a garin Ijebu-jesa, Aregbesola wanda shi ya yi gwamna tsawon shekaru takwas sannan ya sauka Gwamna Gboyega Oyetola ya gaje shi, ya ce ya amince da Oyetola ya zama gwamna ne bayan Tinubu ya bada shi a matsayin wanda ya ke so ya gaje shi, kuma ya yi alƙawarin zai ɗora kan ayyukan raya ƙasa da Aregbesola ya kafa a Osun.
“Amma Oyetola na hawa a 2018 kujerar gwamna, sai ya kauce, ya saki hanya, ya shiga daji kuma ya karya alƙawari.”
Daga nan sai Aregbesola ya ce “kamar yadda Tinubu da mutanen sa su ka yi wa tsohon Gwamnan Legas Akinwunmi Ambode saboda ya saki hanya, su ma a Jihar Osun haka za su yi wa Oyetola tunda ya saki hanya.”
“Kamar yadda aka yi a Legas, mu ma a Osun za mu yi amfani da ƙuri’u mu watsar da mugun irin da aka dasa mana, maras cika alƙawari.” Inji Aregbesola.
“Ku je ku shaida masu mu ke da jam’iyyar nan. Kuma mu ne ‘yan Afenifere na gidi. Mu ke ƙyanƙyasar Awolowo da Bola Ige.
“Wannan jam’iyya APC ta mu ce, mu ba ‘ya’yan bora ba ne.”
Can da jawabi ya yi zafi, Aregbesola ya fito ƙuru-ƙuru ya na ragargazar Tinubu da Gwamna Oyetola, har ya na yi masu waƙa da Yarabanci, ya na cewa, “adabo da gayyar tsiya.”
“Yanzu mun dawo gida domin mu ɗora jam’iyyar mu a kan hanya, ta yi saitin tafiya sosai a kan miƙaƙƙar hanya.
“Mun bi mutumin nan, mun yi tsammani nagari ne. Wasu ma har ƙoƙarin fitar da mu daga Musulunci su ka yi don mun bi shi. Mun riƙe shi amana babu sharri, amma ba mu sani ba ashe shi sharri ya ke ƙulla mana.
“Mun kai shi inda Ubangiji bai kai shi ba. Shi kuma ya riƙa ɗaukar kan sa kamar wani ubangijin bautar mu.
“Mu kuma mun rantse sai mun tozarta duk wani da ya ɗauki kan sa tamkar ubangiji.
“Mu muka gina wannan jam’iyya bayan mun sha wahala da gumi har wasu da dama mun rasa su. Mun hau mulki ranar 27 Ga Nuwamba, 2010. Mun yi mulki shekaru takwas, a bisa adalci kamar yadda Allah ya ce mu yi adalci. Kuma jama’ar Osun sun ji daɗin mulkin mu.”
Ko Bira’izan Osinbajo Za Su Iya Tarwatsa Tsatsube-tsatsuben Tinubu A Kiɗin Garayar 2023?:
Ya kamata a kyautata wa Osinbajo zato cewa bai taɓa fitowa ya nuna buƙatar tsayawa takarar shugabancin Najeriya, domin ya gaji Shugaba Muhammadu Buhari a 2023 ba.
Sai dai kuma ko makaho ya shafa hoton Osinbajo, zai iya rantsewa ya na son kujerar. Ba don komai ba, sai saboda shi ne na biyu ga Shugaba Buhari, kuma ya fi kowa kusanci da kujerar, baya ga mai ita a yanzu, wato Buhari ɗin.
Ba ɓoyayyen abu ba ne ga kowa a ƙasar cewa Osinbajo yaron Tinubu ne. Kuma Tinubu ɗin ne ya amince ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa, amma ba don ya so ba, saboda kawai an ƙi amincewa Tinubu ya zama Mataimakin Buhari a zaɓen 2015.
Sannan kowa ya san Tinubu ya fi Osinbajo maita da kwaɗayin son zama shugaban ƙasa.
Haka kuma ƙungiyoyi daban-daban sun fito su na kaɗa gangunan neman Osinbajo ya fito takara, su na kashe maƙudan kuɗaɗen kamfen, zirga-zirga da tuntuɓa. Babu wanda ya san mai ɗaukar nauyin su, domin dai hatsi a gona ba ya kai kan sa cikin gari, sai wani ya ɗauka ya kai shi.
Har yau Osinbajo bai nesanta kan sa daga masu neman ya fito ba, kuma bai taka masu burki ba. Su kuma sai ƙara ƙarfi su ke yi, daga sama har ƙasa.
Bayanan ƙadda-ƙanzon-kuregen da ake yaɗawa a cikin ƙasar nan na nuna cewa an fi son Osinbajo ya fito fiye da TInubu. Shi kuma Tinubu har yau saboda yakana kuma ya na kan mulki, bai kai ga bayyana ra’ayin sa ba tukunna.
Duk da cewa sai cikin watan Yuni ake sa ran APC za ta yi zaɓen fidda-gwani, kuma sai cikin Agusta za a rufe ƙofar karɓar ɗan takara, wasu abubuwa da su ka faru, musamman iƙirarin da Babban Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Siyasa, Babafemi Ojudu ya yi, inda ya nuna bijire wa tsohon ubangidan sa Tinubu, ya koma bayan Osinbajo a 2023, hakan ya nuna cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa ya shirya wani abu a ɓoye. Kuma da ƙarfin sa zai fito idan ya tashi fitowa, tamkar fitar harsashen bindiga.
Me Osinbajo Ya Taka Ne Har Yaron Sa Ojudu Ya Yagalgala Rigar Tinubu?
Na Fi Ƙarfin Wasu ‘Yan Iska Su Rirsasa Ni Bin Tinubu A Zaɓen 2023 -Ojudu, Mashawarcin Buhari:
Yayin da aka fara kaɗa gangar zaɓen 2023, kuma har wasu jiga-jigai sun fara karkarwa su na kirari, ɗaya daga cikin wanda ya nuna maitar neman tsayawa takara a ƙarƙashin APC, shi ne jagoran jam’iyyar Bola Tinubu.
To sai dai tun tafiya ba ta ma kai ga batun fitowa yankan tikitin takara ba, Tinubu ya fara haɗuwa da cikas.
Wasu da aka riƙa danganta su da Tinubu sun riƙa fitowa su na ƙaryatawa, musamman Ƙungiyar Yarabawa Zalla (OPC), Dele Mamudu da wasu daban.
A jiya kuma Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhari a kan Al’amurran Siyasa, Babafemi Ojudu, ya fito ya bayyana cewa ba zai goyi bayan kamfen ɗin ubangidan sa Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa ba.
Ojudu wanda yaron Bola Tinubu ne a baya, ya ce amma fa kada jama’a su ka matsayar da ya ɗauka a matsayin cin amana.
Cikin Wata sanarwar da ya fitar a shafin sa na Facebook a ranar Talata, Ojudu wanda ya ce shi da Tinubu sun daɗe su na tafiya tare, “to amma a gaskiya mutunci na da tunanin da zuciya ta ke nuna min, ba daidai ba ne na goyi bayan Tinubu ya zama shugaban ƙasa.”
Ojudu da Tinubu sun fara shaƙuwar siyasa tun farkon 1990, inda tsohon gwamnan Lagos ɗin da kuma ɗan jarida Ojudu, wanda ya koma ɗan siyasa ya zama sanata.
Tinubu ya narka kuɗi a mujallar TheNews, wadda mallakin Ojudu da wasu abokan sa ce a lokacin.
Sai dai kuma a cikin 2016, Buhari ya naɗa Ojudu Mashawarcin Shugaban Ƙasa a Harkokin Siyasa, kuma ya umarce shi da ya yi aiki tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo.
Duk da cewa Tinubu ne tsanin da aka taka aka ɗora Osinbajo kan kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa, tun tafiyar ba ta yi nisa ba su ka raba hanya, babu jituwa a tsakanin su.
Ana ganin dai a yanzu Ojudu ya ɗauki hanyar goyon bayan takarar Osinbajo, kuma ya fara tallar sa a zahiri da baɗini.
A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, tsohon sanatan ya ce har an fara yi masa barazana, kuma iyalin sa ma ana yi masu barazana, saboda kawai matsayar da ya ɗauka ta ƙin mara wa Tinubu baya.
“Kada ma wani ya yi tunanin cewa zai iya tirsasa ni yin abin ca mutunci na da zuciya ta ba su amince min na yi ba.” Inji Ojudu.
“Masu yawan kiran waya ta su na yi min barazanar banza da wofi da masu neman su kunyata iyali na, su daina haka nan.
“Na san Tinubu. Ina girmama shi. Da yawan waɗanda ke goyon bayan sa a yanzu, ba su ma san wane ne Tinubu ba. Da sun san wane ne Tinubu da ba su tsaya su na tayar da jijiyar wuya a kan sa, har su na neman ci min mutunci ko kai min hari ba.
“Lokacin da Tinubu ya ƙi goyon bayan takarar Obasanjo a 2003, ba a kira shi maci amanar jinsin Yarabawa ba ko maci amanar Afenifere.
“Ya zaɓi abin da ran sa ya biya masa a lokacin, kuma tarihi ya yi masa hukunci da alƙalanci. To ni ma ina so tarihi ya yi min hukunci da alƙalanci.
“Kuma lokacin da Tinubu ya goyi bayan Olu Falae maimakon jagoran mu Bola Ige, ai babu wanda ya kira shi Tinubu ɗin maci amana.
“Ku kuma ƙananan ‘yan iskan da ke ta aiko min da saƙonnin waya ku na yi min barazana, ni da iyali na, kuma ku na surfa min zagi don na ƙi goyon bayan Tinubu, ku sani hakan ba dimokraɗiyya ba ce.
“Na shafe shekarun tasowa ta a rayuwa ina yaƙi da danniya da masu danniya da masu mulkin soja. To har yanzu a shirye na ke, kuma ba zan saki abin da zuciya ta ta fi kwantawa da shi ba, ko da kuwa za a ɗauki rai na.”
Kusancin Osinbajo Da Kujerar 2023:
Ganin yadda wasu a yanzu ke gwasale Atiku da Tinubu, su na cewa tunda sun tsufa su haƙura da takara, hakan alamomi ne na share wa irin su Osinbajo hanya.
Musanman ma shi Osinbajo ɗin wanda ya fi kowa kusa da kujerar. Tsalle ɗaya kaɗai zai yi ya dira a kan ta.
Discussion about this post