Dan majalisar tarayya mai wakiltar Birnin Kudu/Buji jihar Jigawa na Jam’iyyar APC, Magaji Da’u, ya raba kekunan guragu 20 ga wasu nakassau a fadin jihar.
A jawabin da yayi a wajen rabun wadannan kekuna Honorabul a kauyen Gantsa ranar Lahadi ya bayyana cewa ya yi haka ne domin ya taimakawa wa nakasassu musamman wadanda suke zuwa makaranta su samu sauki wajen zirga-zirgar Karatu.
Dan majalisan ya kuma aza tubalin ginin asibitin mata domin mata masu ciki da kananan yara a karamar hukumar Buji.
Da’u ya mika godiyarsa ga jama’ar mazabarsa da gwamnatin jihar Jigawa bisa goyan baya da suke bashi a koda yaushe.
Ya ce wadannan ayyuka da yake kaddamarwa na daga cikin alkawuran da ya dauka wa mutanen sa a lokacin da yake neman zabe. Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba zai kaddamar da wasu ayyukan da yayi a karamar hukumar Birnin Kudu.
Ayyukan da Honarabul Da’u ya kaddamar a karamar hukumar Buji sun hada da gina hanya a Gubunbiya da Jaka masu tsawon kilomita 6, kwalbati, magudanan ruwa da rijiyoyin burtsatse a kauyukan Yayarin Tukur da Gofara.
Ya kuma kaddamar da ginin koyan na’urar Komfuta a Gantsa, ajujuwa uku a makarantun firamaren dake kauyukan Kwalele, Kukuma da SaguSagu tare da bada takardun rajistan dalibai guda 1,000.
Da’u ya kuma dora tubalin gina wurin koyan na’ura maikwakwalwa a makarantar sakandare na JSS Buji da tubalin gina makarantar Islamiya a kauyen Karanjau.
Da yake tofa albarkacin bakin sa awurin taron dan majalisa mai wakiltar Buji a majalisar jihar Sale Baba da shugaban karamar Buji Abdullahi Muhammad sun yabawa Da’u bisa wadannan manyan ayyuka da ya yi wa mutanen da suka zabe shi.
Gwamnan jihar Muhammad Badaru wanda mataimakinsa Umar Namadi ya wakilce shi a wajen taron ya yi kira ga mutane a jihar da ci gaba da mara wa jami’iyyar APC bayan domin ci gaba da kwankwadan romon dimokardiya a kasar nan.
Sai dai kuma da yake abu ce ta siyasa, an dan samu miskila a lokacin da dan majalisar ya wuce ta kauyen Kukuma, kamar yadda wasu wadanda abin ya auku a gaban su suka sanar wa PREMIUM TIMES HAUSA.
An samu rahoton wasu hasalallun matasa sun yi kokarin tada husuma a lokacin da dan majmalisar ya wuce ta wannan gari. Sun rika jifa suna kona kara a bakin titi suna cewa basu so.
Binciken PREMIUM TIMES Hausa ya nuna cewa wasu yan adawar siyasa ne da magoya bayan su suka harzuka a lokacin amma kuma jami’an tsaro sun tarwatsa wadannan matasa.
‘Yan sanda sun shaida wa Premium Times Hausa cewa ɗan majalisar yana kan hanyarsa ta zuwa wani taron siyasa ne a yankin lokacin da abin ya faru.
Mai Magana da Yawun Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Jigawa, Lawan Adam, yace ba ‘yan bindiga ne suka kai harin ba, rashin fahimta ce kawai tsakanin wasu ɓangarorin siyasa ya haifar da harin.