Wasu yara kanana biyu sun rasa rayukansu bayan sun yi ‘Alkafira’ cikin shirgegen dam din dake wurin shaƙatawa na Rayfield Resort a garin Jos jihar Filato.
Wani da abin ya auku a idon sa Gyang Pwol ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Lahadi cewa yaran sun fada cikin dam din tun ranar Asabar ne.
Ya ce yaran Michael Nyam mai shekara 8 da Elijah Solomon mai shekara 6 sun fada cikin dam din domin ciro takalmin wani abokinsa da suka faɗa ruwan.
Sai dai kuma da yake abun ya zo a kan gaɓa wato ajali waɗannan yaran basu fito da ransu ba.
Pwol ya ce duka yaran mazaunan Rayfeild ne kuma tuni har an yi jana’izan su.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ubah Ogaba ya ce rundunar ba ta masaniyar abin da ya faru domin babu wanda ya sanar da ƴan sanda abinda ke faruwa.
Discussion about this post