A ranar Alhamis ɗin nan, PREMIUM TIMES Hausa ta buga wata gagarimar gadangarƙamar cefanar da kadarorin da Hukumar AMCON ta yi, har na Naira Biliyan 114.5.
Wannan ya sa wannan jarida ta yi waiwayen wasu manyan labarai huɗu da ta buga cikin 2021 da 2022 waɗanda duk batutuwa ne da su ka danganci sayar da kadarorin Gwamnantin Tarayya, da ake zargin akwai badaƙala a ciki.
Ranar 21 Ga Janairu 2021:
Majalisar Tarayya Ta nemi Ba’asin Yadda Aka Yi Da Kadarorin Da Aka Ƙwato Daga Tsoffin Shugabanni:
Majalisar Tarayya ta nuna damuwa dangane da rashin sanin haƙiƙanin yadda aka yi da kadarorin da aka ƙwato daga tsoffin shugabannin ƙasar nan.
Kwamitin Lura da Kadarorin Gwamnantin Tarayya ne ya bayyana haka a lokacin da Babban Sakataren Kwamitin Ƙwato Kadarorin Gwamnanti a Hannun Ɓarayin Gwamnati (PIC), Bala Samid ya bayyana a gaban kwamitin a ranar Litinin.
Shugaban Kwamitin Majalisa Honorabul Ademorin Kuye, ya bayyana cewa sun gano cewa wasu kadarorin da aka ce an sayar, to ba a sayar da su ba.
Kuma kwamiti ya gano wasu gidajen da aka sayar ɗin har yanzu ba a biya kuɗaɗen ba.
Musamman kwamitin ya nemi a kawo masa bayanai dalla-dalla dangane da yadda aka yi da kadarori ko kuɗaɗen da aka karɓo waɗanda tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha ya kimshe a ƙasashen waje, sai daga baya lokacin wannan gwamnatin aka riƙa maido kuɗaɗen.
Kuye ya kuma ɗora alamomin tambaya akan yadda aka sayar da wasu kadarorin.
Ya ce sun gano har yanzu wasu akwai jama’a a ciki, ba su fita ba, alhali an shaida masu cewa gidajen babu kowa a cikin su.
Kwamiti ya kuma nemi sanin adadin kuɗaɗen da aka sayar da kadarorin, tare da gabatar masa da shaidar ko nawa aka saka a aljihun gwamnatin tarayya.
Babban Sakataren Kwamiti Bala Samid ya ce gidajen da har yanzu mazaunan su ba su tashi ba, sun kasa biyan haya ne, kuma a duk lokacin da aka yi ƙoƙarin fitar da su, sai su je kotu su samu umarnin hana fitar da su da tsiya daga kotuna daban-daban.
Ya ce ya na maraba da duk wani mataki da Majalisar Tarayya za ta ɗauka, domin a karɓo kuɗaɗen hayar da mazauna gidan su ka ki su biya.
Ranar 20 Ga Janairu 2022:
Yadda Kotu Ta Ci Tarar Ɓarayin Ɗanyen Man Naira Miliyan 200 Tarar Naira Dubu 20, Aka Sallame Su:
Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya ta Warri, da ke Jihar Delta, Okon Abang, ya yanke hukuncin da ran sa bai so ba ko kaɗan, amma kuma babu yadda zai yi.
Abang ya yanke wa mutum 9 da ya samu da laifin satar ɗanyen mai suka loda a jirgin ruwa, har na naira miliyan 200, hukuncin biyan tarar naira 2,000 kowanen su.
Sannan kuma aka ci su tarar naira miliyan biyar kuɗin fansar jirgin ruwan su na dakon ɗanyen mai wanda aka kama su tare.
Mutanen dai an kama su ne a ranar 11 Ga Nuwamba 2015, lokacin da Sojojin Ruwan Najeriya ke sintiri. An kama su a cikin jirgin ruwan da suka saci ɗanyen man su ka loda.
Sojojin Ruwan Najeriya ne su ka kama su, sannan su ka damƙa su ga Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.
Bayan an tsananta bincike, an gano mutanen sun daɗe su na satar ɗanyen man Najeriya.
Daga nan kuma Ofishin Antoni Janar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ya karɓe binciken, inda a ranar 8 Ga Afrilu, 2016 aka gurfanar da mutum 9 a cikin mutum 13 da aka kama, aka saki mutum uku.
Mai Gabatar Da Ƙara Ta Koma Gabatar Da Shiririta:
An fara shari’a tiryan-tiryan Amma daga baya, sai mai gabatar da ƙara daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya, Onyeka Ohakwe ta shigar da sanarwar yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin waɗanda ake tuhumar da kuma Gwamnatin Tarayya, wato ‘plea bargain’.
A tsarin ‘plea bargain’, ɓarawon kayan gwamnati zai ajiye kayan da ya sata, ko ya biya kuɗin da ya wawura, sannan a yi masa sassaucin hukunci.
Yayin da aka zo yanke hukunci, Mai Gabatar da ƙara a ranar 27 Ga Oktoba, 2021 ta shaida wa kotu cewa ai an yi yarjejeniyar ‘plea bargain’ da ɓarayin su da gwamnati. Wato hakan na nufin tilas kotu ta yi masu sassauci kenan wajen yanke masu hukunci.
Yadda Mai Gabatar Da Ƙara Ya Rufta Mai Shari’a Cikin Rijiya:
Jikin Mai Shari’a Okon Abang ya yi sanyi laƙwas, ganin yadda aka nunke shi baibai, ta yadda zai jingine tsatstsauran hukuncin da ya yi niyyar danƙara ɓarayin, wanda zai iya kai shekaru masu yawan da sai sun mutu a kurkuku kafin wa’adin fitar su ya cika.
Abang da ya karanta sabon cajin da ake wa ɓarayin, zuciyar sa ta ɓaci, amma babu yadda ya iya, tunda alƙali na yanke hukunci ne bisa duba da irin tuhumar da mai gabatar da ƙara ya gabatar masa.
“Wannan wace irin yarjejeniya ce kuma babu daɗin ji ko kaɗan? Maimakon a ƙara tsaurara masu tuhuma, sai a sassauta?
“Irin waɗannan mutanen fa kamata ya yi a ɗaure su har igiya ta yi rara, ba a sassauta masu tuhuma su ci bilis ba.” Inji Mai Shari’a Abang.”
Abang dai ya yanke masu hukuncin tarar naira 2,000 kowanen su mutum 9. Sai jirgin ruwan na su wanda a shari’a ƙwace shi ya kamata a yi, amma sai aka ce su biya tarar naira miliyan 5 kacal a sakar masu jirgin su.
‘Banza Ta Kori Wofi: Ɓarayin Da Gwamnati Ta Yi Wa Gata A Kotu, Ba Da Son Ran Mai Shari’a Ba:
Ɓarayin ɗanyen man har metrik tan 4,000 sun haɗa da:Adeola Goodness, Olaoluwa Temitope, Kelvin Onyeka, Dare Likman, Ibrahim Sese, Amaechi Nkwocha, Anayo Chukwu, Emmanual Ekwuma da Lucky Urhie.
An kama su da lodin ɗanyen mai cike da tankar jirgin ruwa a jihar Delta. Tankar jirgin ruwan dai ta na da lamba 7323473.
Mai Shari’a ya yi ƙorafin cewa tsatsauran hukunci ya kamata a yanke masu, saboda su na yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, kuma abin da su ka sata zai iya saisaitawa da sauƙaƙa wa ɗimbin ‘yan Najeriya ƙuncin rayuwa.
Abang ya ce ba haka ake yaƙi da cin rashawa da masu karya tattalin arzikin ƙasa ba.
Ranar 1 Ga Janairu, 2022:
Yadda Ministan Shari’a Ya Bayar Da Kwangilar Tantance Kadarorin Gwamnati A Asirce:
Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayar da kwangilar tantance kadarorin gwamnatin tarayya na biliyoyin nairori ga wani kamfani da lauyoyi a asirce.
Kamfanin da ya taki sa’ar wannan gadangarƙamar dai sunan sa Gerry Ikputu & Partners, wanda kuma kamfanin tantance darajar farashin maka-makan rukunin gidaje ne, wanda shi ma ya tattago wani kamfanin lauyoyi mai suna M. E. Sheriff & Co, a matsayin ejan ɗin kwangilar.
Kashe Mu Raba Ba Sata Ba, Almundahana Ce:
Minista Malami ya umarci kamfanin ya binciko yawan filaye, gonaki da maka-makan gine-ginen Gwamnatin Tarayya a waɗansu jihohi 10 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
2. Za su ɗauki kashi 3 bisa 100 na ilahirin kadarorin da su ka gano.”
Haka dai yarjejeniyar kwangilar ta ƙunsa, wacce aka yi a asirce, kuma mai ƙunshe da ƙa’idojin sirri cewa kada su kuskura su bayyana wa jama’a kwangilar.
3. Sharuɗɗan da aka rattaba sun ce kada ‘yan kwangilar su bayyana wa bainar jama’a aikin kwangilar, ba tare da umarnin Ministan Shari’a Abubakar Malami ba.”
4. Amma kuma an gano cewa Sashen Bincikowa da Tantance Kadarorin Gwamnatin Tarayya na Ma’aikatar Shari’a wanda aka umarta su yi aikin tare da kamfanonin, ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka rattaba ɗin duk bige ce kawai da bagaraswa, ba sahihiya ba ce.
Malami ya bayar da kwangilar ga M. E. SHeriff & Co cewa ya gano tare da tantance kadarorin a cikin watanni shida.
Adadin kwanakin watannin da Malami ya bai wa kamfanin dai zai ƙare a cikin watan Afrilu. Haka dai yarjejeniyar kwangilar da aka rattaba a ranar 5 Ga Oktoba, 2021 ta nuna.
Malami ya umarci kamfanonin su riƙa kai masa rahotannin yawan adadin abin da suka gano a duk wata.
Irin Kadarorin Da Aka Kafa Wa Kahon-zuƙa:
Wasiƙar yarjejeniyar ta faɗo hannun PREMIUM TIMES. An rubuta ta a ranar 5 Ga Oktoba, 2021, ta ƙunshi shi jerin sunayen kadarorin da za a tantance a jihohi 10 da Abuja.
Kadarori 74 ne ake so a binciko tare da tantance su a Legas, Ribas, Akwa Ibom, Cross Riba, Abia, Anambra, Edo, Enugu, Imo da Delta.
PREMIUM TIMES Hausa na da jerin sunayen kadarorin da ake so a gano har 74, waɗanda daga ji da gani za a san cewa kamfanonin ba wani jan aiki ne za su yi ba, domin kowane gini ko fili akwai adireshin wurin da ya ke.
Haka kuma ganin sunayen sauraren zai sa mai karatu ya gane cewa kamfanonin za su kuɗance idan aka ba su kashi 3 bisa 100 na yawan kadarorin.
Yarjejeniyar dai ta nuna ba za a biya su kashi 3 ɗin ba, har sai bayan sun kammala aikin na su.
Babban Lauya Itse Sagey ya ce wannan kwangila haramtacciya ce, domin bai kamata a bai wa wani kamfani aikin ganowa da tantance kadarorin gwamnatin tarayya ba, alhali ga hukumomin Gwamnantin Tarayya irin su EFCC da ICPC, waɗanda su ne ya dace a bisa tsarin doka su yi aikin.
Ranar 1 Ga Disamba 2021:
Minista Malami Ya Kafa Kwamitin Binciko Waɗanda Ake Zargi Sun Fara Sayar Da Kadarorin Da Aka Ƙwato Daga Hannun Ɓarayin Gwamnati:
Ministan Shari’a Abubakar Malami ya kafa Kwamitin Bankaɗo Waɗanda Su Ka Fara Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya, waɗanda aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati.
Kafa kwamitin ya biyo bayan ɓullar wasu rahotanni a jaridu da su ka ce wasu a cikin Ma’aikatar Harkokin Shari’a sun fara sayar da kadarorin da gwamnatin ta ƙwato a ɓoye ta ƙarƙashin ƙasa.
Cikin wata takardar da Kakakin Malami ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ya ce, “Ministan Shari’a Abubakar Malami bai bada iznin a fara sayar da kadarorin ba. Kuma idan ma har wasu sun aikata laifin sayar da wasu daga cikin kadarorin, to ba da iznin sa ba.”
Gwandu ya ce a kan haka Malami ya kafa Kwamitin Mutum 5, da za su binciko tare da gano waɗanda ke da hannu wajen sayar da kadarorin, idan har an sayar da wasu ɗin.”
Kwamitin na ƙarƙashin shugabancin Daraktan Shigar Da Ƙararraki na Tarayya (DPP), sai kuma Babban Sakatare a Ma’aikatar Shari’a a matsayin sakataren kwamiti.
An bayar da mako ɗaya duk mai wata hujja ko ƙarin haske kan wannan zargi, to ya gaggauta aikatawa a Ofishin DPP ko Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a, daga ranar 1 Ga Disamba zuwa 7 Ga Disamba.
“Kwamiti zai bincika ya gano idan har an fara sayar da kadarorin ta ƙarƙashin ƙasa.
“Idan ya gano an fara, to zai bankaɗo duk wani ko wasu masu hannu a cikin wannan harƙalla.
“Kadarorin da za’a yi binciken a kan su, sun haɗa da gidaje, maka-makan filaye, motocin alfarma, tankokin jiragen ruwa na ɗaukar dakon fetur, masana’antu da manyan injinan sarrafa kayayyaki a cikin masana’antun da gwamnati ta ƙwace.
Watan Nuwamba, 2021:
Gwamnoni 36 Sun Maka Gwamnatin Buhari Kotun Ƙoli, Su Na Cigiyar Naira Tiriliyan 1.8 Waɗanda Aka Ƙwato Daga Hannun Ɓarayin Gwamnati:
Gwamnonin Najeriya su 36 sun maka Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari Kotun Koli, su na zargin Buhari ya karkatar da kuɗaɗen da aka ƙwato daga ɓarayin gwamnati har naira tiriliyan 1.8, sai kuma kadarorin da aka ƙwaro na naira biliyan 450.
Gwamnonin dai sun yi zargin cewa Gwamnatin Buhari ta danƙara kuɗaɗen cikin Asusun Tara Kuɗaɗen Shigar Gwamnatin Tarayya, wato ‘Consolidated Revenue Account’ (CRA), wanda yin hakan kuwa babban laifi ne, kuma take Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ne ƙarara.
Gwamnonin 36 sun shaida wa Kotun Ƙoli cewa, dokar tsarin mulkin Najeriya cewa ta yi a tara kuɗaɗen da kadarorin a ƙarƙashin Asusun Tara Kuɗaɗe Da Kadarorin Sata Na Gwamnatin Tarayya, wato ‘FGN Assets Recovery Account’ (FGNARA) da ke a Babban Bankin Najeriya.
A cikin kwafen ƙarar da su ka shigar, sun ce abin da gwamnatin Buhari ya yi ya karya dokar ƙasar nan ƙuru-ƙuru.
“Asusun Gwamnantin Tarayya nan ne ya wajaba a tara kuɗaɗen a cikin Asusun Tara Kuɗaɗen Sata, Babban Bankin Najeriya. Saboda shi ne asusun da doka ta yarda a riƙa raba kuɗaɗen da ke ciki tsakanin Tarayya, Jihohi da Ƙananan Hukumomi.
“Shi kuma Asusun Tara Kuɗaɗen Shigar Gwamnatin Tarayya na CRA, asusu ne kawai na tara wa gwamnatin tarayya kuɗaɗen shiga da su ka haɗa da kuɗaɗen harajin da lasisin da gwamnatin tarayya ke karɓa, kuɗaɗen harajin filaye da gonaki, kuɗaɗen ruwa da gwamnatin tarayya ta karɓa daga waɗansu hannayen jarin ta da sauran su.”
Babban Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya 36 (NGF), Asishanu Okauru ne ya bayyana haka a cikin kwafen takardar da ya maka Gwamnantin Tarayya ƙara, a madadin ƙungiyar gwamnonin.
“Abin da Gwamnatin Buhari ta yi ya saɓa wa Sashe na 162 (1), 162 (10) da kuma Sashe na 80 na Dokar Kuɗaɗe ta 1958.” Inji Okauru.
Ya ce dukkan waɗannan sassa sun nuna cewa a Asusun Gwamnantin Tarayya za a riƙa ajiye dukkan kuɗaɗen da aka karɓo daga ɓarayin gwamnati, a cikin Asusun Bai Ɗaya Na Gwamnatin Siriya.
Gwamnonin Najeriya 30 Sun Nemi Kotun Ƙoli Ta Tilasta Wa Shugaba Buhari:
1. Ya maida naira tiriliyan 1.8 daga Asusun CRA da kuma Kadarorin naira biliyan 450 duk zuwa cikin Asusun FGNARA da ke cikin Baban Bankin Najeriya, CBN.
2. Sun buƙaci Kotun Ƙoli ta tilasta wa Shugaba Buhari bayyana dalla-dallar adadin kuɗaɗen da aka ƙwato a hannun ɓarayin gwamnati, waɗanda bai saka a Asusun Gwamnantin Tarayya ba.
3. Kotun Ƙoli ta tilasta wa Hukumar Raba Kuɗaɗen Gwamnatin Tarayya (RMFAC), ta tsara yadda za a riƙa raba kuɗaɗen Gwamnanti tsakanin Tarayya da Jihohi da Kananan Hukumomi.
Babban Lauya kuma fitaccen nan Femi Falana ke jagorantar lauyoyin Gwamnonin Jihohi su 36.
PREMIUM TIMES ta samu kwafen ƙarar wadda aka shigar tun a ranar 16 Ga Yuni, 2021. Yayin da Ministan Shari’a Abubakar Malami wanda shi aka shigar ƙarar, ya ke kare gwamnatin tarayya, a ƙarar mai lamba SCN/CV/393/2021.
Yadda Gwamnonin Najeriya 36 Su Ka Gano Buhari Ya Karya Dokar Ƙin Ajiye Kuɗaɗen:
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya jagoranci gungun wasu ƙwararrun lauyoyi, tare da goyon bayan dukkan Gwamnonin Najeriya su 36. Sun gano cewa an karkatar da kuɗaɗen a Asusun CRA, maimakon a ajiye su a FGNARA.
Sun nuna damuwar su dangane yadda Buhari, mutumin da ke yawan cewa yaƙi da cin hanci da rashawa, amma kuma ya ke tauye wa jihohi haƙƙin da dokar kuɗaɗe ta bai wa jihohin.
Sannan kuma sun nuna Buhari na ƙin bin sharuɗɗa, dokoki da ƙa’idojin da Gwamnatin Tarayya ta shimfiɗa wajen yi wa Asusun FGNARA da Asusun CRA karan-tsaye.
Sun bayyana wa Kotun Ƙoli cewa kuɗaɗen da su ke so Buhari ya maida a Asusun Gwamnantin Tarayya na Bai Ɗaya Da Jihohi, sun tashi naira tiriliyan 1, 836, 906, 543, 658.78.
Kuɗaɗen dai an ƙwato su a hannun ɓarayin gwamnati da sauran masu laifi daban-daban daga 2015.
Sannan kuma su na neman kason jihohin su a cikin kadarorin naira biliyan 450 da aka ƙwato tun daga 2015.
Discussion about this post