Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa ba shi da wani zaɓi, tilas ce ta sa ya kai hari Ukraniya, domin ya hana ƙasar haddasa dalilin da zai sa wasu ƙasashe su mamaye Rasha nan gaba.
Putin ya ce ƙofar tattaunawa a buɗe ta ke, amma ko kaɗan ba zai taɓa yarda Ukraniya ta ƙulla ƙawance da ƙasashen da ba su da wata aniya a duniya, sai ta neman ganin bayan durƙusar da Rasha.
Da ya ke jawabi yayin taro da manyan ‘yan kasuwar Rasha, jim kaɗan bayan fara kai hari a Ukraniya, Putin ya ce ba mamaye Ukraniya ya yi ko zai yi ba, amma ya dai yi amfani da ƙarfin soja ne domin ya hana ƙasar cimma duk wasu manufofin da gwamnatin ƙasar da ɓullo da su da gangan, domin karya ƙasar Rasha a fakaice.
“Na yarda a zauna ta cimma sasanci ta hanyar diflomasiyya. Amma fa ba zan taɓa yin wasarere da duk wata shegantakar da Ukraniya ko gungun wasu ƙasashe za su zo su yi a kan iyakar Rasha da nufin cutar da Rashawa ba. Wannan kam sai inda ƙarfin mu ya ƙare.” Inji Putin.
A wani taƙaitaccen sharhi da Premium Times Hausa ta yi, ta yi dalla-dallar salsala da musabbabin rikicin ƙasashen biyu.
Yayin da aka shiga rana ta biyu ta hare-haren da Rasha ke kaiwa cikin Ukraniya, PREMIUM TIMES Hausa ta yi nazarin musabbabin rikicin na su, domin mai karatu ya tantance inda gaskiya ta ke…
1. Ukraniya yanki ce a cikin Rasha, lokacin da Rasha ke Tarayyar Sobiyet (USSR).
2. Ukraniya da bi sahun wasu yankuna da dama ta ɓalle daga Rasha, ta zama ƙasa mai ‘yancin kan ta cikin 1991.
3. Ukraniya ta bi sahun wasu ƙasashe irin ta na Turai ta Gabas, ta nemi shiga ƙawance Ƙungiyar NATO ta ƙasashen Turai ta Yamma da Amurka.
4. Ukraniya ta tattago ƙasashen Turai na Yamma gadan-gadan, waɗanda Rasha ke ganin cewa barazana ne ga ita Rasha ɗin da gwamnatin Vladimir Putin.
5. Kafin ɓallewar Ukraniya, yanki ne mai arzikin noma a Tasha. Amma bayan ya ɓalle, ya fuskanci rigingimun cikin gida, sannan kuma dimokraɗiyya ba ta tsinana masu komai ba sai cin hanci da rashawa, wanda ya hana ta ci gaba.
7. Cikin 2014 Rasha ta mamaye yankin Creamea da ke cikin Ukraniya, yankin da ‘yan ƙabilar Rashawa ne a cikin sa, saboda su na fuskantar barazana daga Ukraniya.
7. Rasha ta goyi bayan ‘yan tawayen Donbas da na Luhansk waɗanda su ka nemi ɓallewa daga Ukraniya, kuma su ka ɓalle, kowane yanki ya kafa ƙasar sa mai cin gashin kan ta.
8. Rasha ta mamaye yankin
Creamea ne bayan an kori shugaban Ukraniya a 2014, wanda ke ɗasawa da Rasha.
Hakan ta sa al’ummar Creamea, waɗanda tushen su na cikin Rasha, su ka fara fuskantar barazanar kisa, tsangwama da cin zarafi.
9. Ganin yadda Ukraniya ke jawo ƙasashen da ke adawa da Rasha a jika, sai ta jibge dakaru 200,000 a ƙarshen 2021, a Belarus, ƙasar da ita ma daga Rasha ta ɓalle, amma su na ɗasawa sosai. Belarus ta yi iyaka da Rasha da kuma Ukraniya.
10. Putin na Rasha ya zargi Shugaban Ukraniya na yanzu Volodymyr Zelenskyy da ƙoƙarin assasa aƙidar Yahudanci ta NAZI a yankin. Putin ya ce Zelenskyy Bayahude ne tun asali.
10. Putin ya ce tilas ya tashi ya kare Gabacin Ukraniya domin ya kare ƙasar sa. Kuma tilas ba zai taɓa barin Ukraniya ta tattago ƙungiyar NATO ba, wadda shigar ta Ukraniya hanya ce ta mamaye Rasha.