Mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar Dattawa ya bayyana wasu dalilai da ya sa ya wancakalar da Jam’iyyar PDP ya koma APC.
Sanata Emmanuel Bwacha wanda daɗaɗɗen ɗan majalisa ne daga jihar Taraba ya bayyana cewa mutanen jihar sa da mazabar sa ne suka bashi wannan shawara ganin yadda jam’iyyar APC ta kantara suntuma-suntuman ayyuka a jihar wanda PDP ba ta yi.
Bwacha da ke wakiltar Taraba ta Tsakiya a majalisar dattawa ya sanar da canja jam’iyyar sa ne daga PDP zuwa APC ranar Alhamis.
Sanatan ya ce akwai wasu ayyuka wanda gwamnatin Buhari ta aiwatar a jihar Taraba da jihar bata taɓa gain irin su ba. A dalilin haka ya ga ta yadda zai saka wa gwamnatin Buhari shine ya tsunduma cikin jam’iyyar domin jihar Taraba ta ci gaba da more lagwadan siyasa karƙashin APC.
Shugaban jam’iyyar na riƙon ƙwarya Mala Buni ya yi wa Bwala iso zuwa fadar shugaban ƙasa domin ayi masa wankan shigowa APC.
Bwacha ya bi sawun sanatoci kamar su Stella Oduah, Elisha Abbo, Peter Nwabaoshi, Muhammed Hasaan, Sahabi Ya’u da Lawali Anka wanda suma duk ƴan PDP ne da amma suka daga tsalle suka tsunduma APC yanzu.
Abin da doka ta ce game da canja sheka daga wannan jam’iyya zuwa wancan
Bisa ga dokar Najeriya duk sanata ko dan majalisar tarayya da ya canja sheka daga wata Jam’iyyar zuwa wata zai sauka daga mukamin da yake kai da kujerar sa a zauren majalisar.
Zuwa yanzu sanatoci da dama sun canja sheka daga jami’iyyar PDP zuwa APC ko daga APC zuwa PDP amma babu wanda ya sauka da kujerar Sanatar sa ko na ɗan majalaisa.