Wasu mazauna garin Benin jihar Edo sun bayyana dalilan da ya sa magidanta ke ajiye farka baya ga matayen su na aure a Najeriya.
A hiran da suka yi da wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN mazauna garin sun ce tarairayar namiji da salon soyayya na daga cikin dalilan da ya sa mazajen aure ke da farka.
Wani dan kasuwa Ojefia King ya ce magidanta kan nemi mata baya ga nasu wanda suka aura saboda samun annashuwan rayuwa ne kawai.
King ya ce mafi yawan mata irin haka basu bukatar komai daga maza illa a kai su yawo sannan da jima’i.
“Wasu matan kan bi mazan aure saboda kudin da sukan samu su biya bukatunsu ne.
Shi kuwa Larry Sideso wanda ke aikin DJ ya ce farka na da dadin sha’ani saboda basu da damuwa sannan burin su su ga sun faranta wa namiji rai.
“Ina da mata kuma ina da farka sannan kowacce ta san matsayinta kuma babu wanda ke shiga hurumin wani.
“Ina son matata fiye da yadda kake tunani amma ina da farka wace ke taya ta wajen biyan bukatuna a duk lokacin da ta gaza.
Wata tela mai suna Richard Amekpa ta ce maigidanta na da budurwa a waje amma kuma saboda kawai saduwa ce ya sa suke tare.
“A soyayya ko aure jima’i, salon soyayya da kula sune ginshikin soyayya da zaman aure.
“Amma idan kana da mata kuma matan naka bata iya gamsar da kai wajen jima’i dole kasamu wata ka ajiye wacce za ta rika share maka hawaye idan bukatar haka ya taso.
“Matata na yawan min rowar saduwa da ita idan bukata ta taso min. Haka nake hakuri in yi ta juyejuye. Ko na lallabata da kyar nake samu biyan bukata. Amma budurwa ta da na kwankwas kofa shi kenan. Na nemi in kara mata amma budurwa ta tace ba sai na kara ba tana nan tare da ni.
Wani malamin Addini yayi kira ga ma’aurata su ci gaba da hakuri da juna maimakon ajiye farka ana abinda bai kamata.