Gwamnan jihar Jigawa Muhammmadu ya bayyana dalilan da ya sa jihar bata fama da hareharen ‘yan bindiga kamar yadda sauran jihohin dake yankin Arewa maso Yamma ke fama da su a kasar nan.
A yankin Arewa maso Yammacin kasar nan mutane da dama sun rasa rayukansu wasu sun rasa gidajen zaman su a dalilin hareharen ‘yan bindiga.
A jihar Zamfara kadai bayanai sun nuna cewa ‘yan bindiga sun karbi sama da naira biliyan uku kudin fansan daga hannun mutane a jihar.
Sannan mata 4,983 sun zama zaurawa, Yara 25,050 sun zama marayu da mutum 190,340 suka rasa gidajen su a dalilin hareharen ‘yan bindiga a tsakanin wannan lokaci.
Sai dai Badaru ya ce duk babu irin wadannan matsaloli a jihar Jigawa domin gwamnatocin da suka gabata a jamhuriya ta hudu sun ci gaba da bin manufar da ta magance tushen ‘yan bindiga a jihar.
Ya ce gwamnati ta samar wa makiyaya burtuloli sannan da yankumam da za su rika kiwo ba tare da sun afkwa wa gonakin manoma ba.
“Gwamnatin Saminu Turaki ce ta fara kirkiro burtuloli da wuraren kiwo tare da sassanta matsalolin manoma da makiyaya tun daga shekarar 1999 zuwa 2007.
“Da Sule Lamido ya zo sai ya gina mashaya wato koramu da makiyaya za su shayar da dabbobin su sannan ya gina musu makarantu.
“Sannan ni kuma da na zo sai na maida hankali wajen inganta abubuwan da na baya suka yi suka bari sannan muka rika aikawa da likitocin dabbobi zuwa rugagen fulani domin yi wa dabbobin rigakafi.
“Dabaran da aka yi ya taimaka wajen hana sacesacen dabbobi, kashekashen mutane sannan kuma da tabbatar da zaman lafiya da ake mora a fadin jihar.
“Idan ma an samu shigowar baki gari mazauna wannan gari da kansu ke sanar da gwamnati domin gudun kada a samu sabani.
Badarau ya ce rashin samar wa makiyaya Fulani ababen more rayuwar na daga cikin dalilan da ya sa ake fama da matsalar ‘yan bindiga.
Discussion about this post