Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamiɗo ya bayyana cewa kwata-kwata ba shi goyon bayan maida muƙaman siyasa zuwa tsarin karɓa-karɓa, saboda babu wata tsiya da karɓa-karɓa ya tsinana wa ƙasar nan.
Lamiɗo wanda ya yi gwamna tsawon shekaru takwas a Jigawa, bayan ya zama Ministan Harkokin Waje daga 1999 zuwa 2003, ya taɓa yin takarar shugabancin ƙasa a 2019.
Jam’iyyar sa wato PDP ta na bin tsarin karɓeɓeniyar shugabancin ƙasa ne tsakanin Kudu da Arewa.
Sai dai kuwa tsohon gwamnan wanda su ne su ka ƙafa PDP, ya shaida wa BBC Hausa a ranar Asabar cewa tsarin karɓa-karɓa bai tsinana komai ba.
“Idan PDP ta zo ta ce a yi tsarin karɓeɓeniyar shugabancin Najeriya, zan ce masu a’a. Saboda yadda duniya aka ci gaba a yanzu, tuni an wuce batun karɓa-karɓar shugabancin. Maganar da ake yi a duniya kawai ita ce yadda za a ci gaba a bunƙasa.
“Ya kamata a ce mu na magana kan yadda za a gina ƙasa da yadda za a ɗinke wuri ɗaya. Na yi amanna za mu iya samun mutumin da zai kai Najeriya gaci, ko daga wace shiyya ko ɓangaren ƙasa ya ke. Don haka mu ma daina maganar bin tsarin karɓa-karɓa a yanzu.” Inji Lamiɗo.
Ya ce a ko yaushe shi ƙasar ce a gaban sa, ba ɓangaranci ba. Shi ya sa ya ke goyon bayan duk ta kowace shiyya ɗan takarar PDP zai fito.
“Ni ban damu ba ko tsayar da Kirista ko Musulmi, ko Bahaushe ko Angas ko Bayarabe. Idan dai zai iya kuma ya cancanta, to a tsayar da shi takara kawai. Mu yi watsi da karɓa-karɓa kawai, domin a baya me ya tsinana wa ƙasar nan?”
Sule Lamiɗo, Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Rabi’u Kwankwaso da Gwamna Aminu Tambuwal na daga cikin ‘yan Arewa da ke neman takarar shugabancin Najeriya.
“Mun Kai Wa Obasanjo Ziyara Don Mu Ceto Najeriya -Lamiɗo:
Da ya ke magana kan ziyarar da su ka kai wa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, wanda tun a cikin 2015 ya keta katin sa na zama mamba ɗin PDP, Lamiɗo ya ce sun kai ziyarar ce domin su ceto Najeriya daga halin ƙuncin da ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya tsunduma ƙasar.
Lamiɗo ya ce Buhari ya ruguza dukkan ayyukan alherin da PDP ta yi a tsawon shekaru 16 da ta yi mulki.
Ya ce mulkin Buhari ya haddasa fatara da yunwa da sabubba na ƙuncin rayuwa.
Ya ce a ziyarar da suka kai wa Obasanjo, sun shafe sa’o’i biyu su na tattaunawa.