Shinkafa ko rice a turance ko kuma oryza sativa yadda ake kiran sa a kimiyance hatsi ne da ake dafawa ko kuma nikawa zuwa gari kafin a ci.
Abincin da kusan kowa ke ci ke nan a Najeriya. Kadan daga cikin irin abincin da ake yi da shinkafa sun hada da Ofada rice, Jollof, tuwon shinkafa, kunun gyada da sauransu.
Tashin farashin shinkafar da aka rika gani a ‘yan shekarun baya nan, ya fara kamari ne bayan da gwamnatin Najeriya ta rufe iyakarta na Seme, wato wanda ke tsakanin Najeriya da jamhuriyar Benin a watan Agustan 2019 don shawo kan matsalar masu fasakwaurin shinkafa ta yadda za ta iya bunkasa noman shinkafa na gida. Sai dai har yanzu farashin na cigaba da tashin gwauron zabi. A halin da ake ciki yanzu farashin buhun shinkafa mai nauyin 50kg tsakanin N23,000 da N30,000.
Ranar Talata 18 ga watan Janairu, 2022, shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da dalar shinkafa miliyan daya da ba’a guma ba a cibiyar kasuwanci da masana’antu a Abuja.
Shirin dalar shinkafar na babban bankin Najeriya ne wato CBN tare da hadin kan Kungiyar Manoman Shinkafa (RIFAN). A cewar wani rahoton gidan talbijin na Channels, ana ganin dalar shinkafar ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.
Mataimaki wa shugaban kasa kan sabbin kafofin yada labarai Bashir Ahmad (@BahirAhmaad) ya rubuta cewa dalar shinkafar ne mafi girma a duk duniya ba nahiyar Afirka ba kawai.
“Shugaba @MBuhari ya kaddamar da dalar shinkafa mafi girma a duniya yau da safe a Abuja” Haka ya rubuta a shafin tiwita.
Bukatar tantance gaskiyar wannan ikirari da Bashir Ahmad ya yi ya sanya Dubawa gudanar da wannan binciken.
Dalar shinkafa da samar da shinkafa
Da muka yi binciken mahimman kalmomi ba mu ga wani abun da ya yi kama da ‘rice pyramid“ ko kuma dalar shinkafa ba, sai dai wadanda aka danganta da rahotannin kaddamar da dalar shinkafar a Najeriya.
Akwai matakai da dama da ake dauka wajen samar da shinkafar ci tun daga yadda ake girbi daga gona zuwa surfa shi da sauransu.
Rahotanni sun ce shugaba Buhari ya kaddamar da dalan shinkafa guda 13, idan aka kirga yawan buhunan da ke cikin kowani dalan ne za’a sami buhuna miliyan daya. ‚yan Najeriya sun saba amfani da buhun shinkafa wanda kan iya kasancewa da nauyin kilogram 50 ko 25. Sai dai ba su saba da shinkafan da ba’a guma ba ko kuma Paddy rice yadda ake kira a turance. To mene ne Paddy Rice?
Paddy rice shi ne shinkafan da ba’a guma ba kuma ba’a surf aba bare a cire daga cikin buntun ba. Bayanan da mu ka samu dangane da yadda ake gwada ingancin shinkafa shi ne a nauyin shi wato tonne ko kilogram ba a girman dalan ba. Dan haka sai muka bukaci mu san nauyin shinkafan da RIFAN ta samu dan ya taimaka mana wajen gano ingancin shinkafan. Sai dai kawo yanzu ba mu riga mun ji daga wurin su ba.
Shi kan shi Bashir Ahmad mun tuntube shi ta hanyar aika masa da sakon text dan jin majiyarsa dangane da furucin da ya yi amma har yanzu ba mu sami amsa daga wurin sa ba.
Bayanai daga sashen kula da noma na Amurka (USDA) sun nuna kasashe 10 da suka fi noma shinkafa a aduniya daga 2016 zuwa 2021, kuma sun hada da China, India, Indonesia, Bangladesh, Vietnam, Thailand, Burma, Philippines, Brazil, Japan. Kasar China ce ke kan gaba inda take noma Tan 148,032 na shinkafa.
Yayin da ba za mu iya samun bayanai kann dalan shinkafa na sauran kasashen duniya dan mu kwatanta da namu ba, bayanan da ake da shi dangane da shinkafa a duniya baki daya, Najeriya ba ta cikin kasashe 10 na farko da ke kan gaba wajen nomawa da sarrafa shinkafa a duniya. Najeriya ce kasa ta 14 a jerin kasahen duniya. Tana noma akalla Tan 5,000 na shinkafar da aka riga aka surfa aka gyara. Babu bayanai dangane da inda aka auna yawan shinkafar da ba’a surfa ba.