Akalla ‘yan bindiga sama da 40 ne aka kashe a ruwan bama-baman da rundunar sojin sama ta yi a jihar Katsina a cikin makon jiya.
Daga cikin ‘yan bindigan da aka kashe akwai Dogo Umaru daya daga cikin yaran shahararren dan bindiga da ya addabi mutane a Zamfara wato Bello Turji.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya a kauyen Magama Umaru da yaran sa sun yi wa motar jami’an tsaro kwantar bauna inda suka kashe DPO sannan soja daya ya ji rauni
Umaru da yaran sa sun sauka a wata makarantar firamaren Tsamben Dantambara inda daga nan suke fitowa suke kai wa mutane hari.
Bayan ruwan bamabaman da rundunar sojin sama ta yi mazauna Tsamben Babare sun ce ‘yan bindiga 42 ne aka kashe inda a ciki akwai Umaru.
Bayan haka wani jami’in rundunar sojin Najeriya da baya so a fadi sunan sa ya ce rundunar sojin Najeriya da sauran jami’an tsaro sun inganta matakan gamawa da ‘yan bindiga a Arewa maso Yammacin kasar nan.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya rundunar sojin sama dake jihar Kaduna da Niger sun kashe ‘yan bindiga da dama a ruwan bama-baman da suka yi a makarantar sojoji dake hanyar Shadadi zuwa Maundu.