Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa har yanzu dai akwai sauran baddalallun hukunce-hukunce da tanade-tanade a cikin Sabuwar Dokar Zaɓe, wadda ya sa wa hannu a ranar Juma’a.
Buhari ya yi bayanin yayin da ya sa wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu, inda yanzu ya zama Sabuwar Dokar Zaɓe.
Ya yi bayanin da sa hannun a gaban Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila da wasu manyan jami’an gwamnati.
Shugaban ya gode wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya, ganin yadda su ka sake yi wa ƙudirin kwaskwarima daidai yadda ya ke so.
Ya ce dokar za ta ƙara inganta martabar zaɓe a Najeriya, musamman ta sabuwar hanyar yin amfani da kayan sadarwa da na’urori na zamani domin tabbatar yin komai ƙeƙe-da-ƙeƙe a lokacin zaɓe.
Ƙorafe-ƙorafen Buhari:
Sai dai kuma Buhari ya yi ƙorafi a kan Sashe na 84(12).
Ga Abin Da Sashen Ya Gindaya:
“An hana duk wani mai riƙe da muƙamin gwamnati wato muƙaman siyasa a Tarayya, Jiha ko Ƙaramar Hukuma ya yi zaɓe ko a zaɓe shi a wurin Taron Gangamin Jam’iyya ko Zaɓukan Shugabannin Jam’iyya na jiha ko ƙaramar hukuma ko tarayya.”
Buhari ya ce wannan sabuwar dokar ta ci karo da wata dokar da ke cikin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
Ya ce dokar ta tauye wa masu riƙe da muƙaman ‘yancin su na yin zaɓe ko a zaɓe su a shugabancin jam’iyyu.
Daga nan sai Buhari ya yi nuni da Sashe na 40 da na 42 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.
“Doka ta amince wanda ke riƙe da muƙamin gwamnati zai iya ajiye aikin sa kwanaki 30 kafin ya tsaya takarar wani muƙamin shugabanincin jam’iyya, wato kafin zaɓen.” Inji Buhari.
Sai dai kuma ya ce duk da wannan cikas ɗin, ya sa wa dokar hannu, saboda la’akari da muhimmanci, ƙurarren lokaci da sauran su.
Yadda Majalisar Dattawa Ta Ƙara Yi Wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Wata Kwaskwarima:
A wani ƙwarya-ƙwarya kuma taƙaitaccen cimma matsaya da Majalisar Dattawa ta yi a ranar Talata, ta sake yi wa Ƙudiri na 84 na Dokar Gyaran Zaɓe Kwaskwarima.
An yi kwaskwarima ɗin ce ta yadda idan Shugaba Muhammadu Buhari ya sa mata hannu, za ta bai wa jam’iyyun siyasa damar kowace ta bi tsarin da ya fi daidai a gare ta wajen zaɓen fidda gwani.
A cikin ƙudirin gyaran dokar zaɓen dai wanda Majalisar Dattawa ta sa wa hannu cikin 2021, sun rattaba cewa zaɓen fidda gwanin kowace jam’iyya zai kasance na ‘yar-tinƙe ce.
Sai dai kuma Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da wannan ƙudirin ba.
Dalili kenan ya maida wa majalisa domin ta yi masa kwaskwarima.
Yayin da Majalisar Dattawa ta amince da zaɓen kai-tsaye ko ‘yar tinƙe ko kuma tsayar da ɗan takara a bisa tsarin yarjejeniyar amincewa, ita kuwa Majalisar Tarayya ba ta amince da fitar da dan takara ta hanyar cimma yarjejeniyar tsayar da mutum ɗaya ba tare da zaɓe ba (wato consensus candidate).
Farkon makon jiya ne Majalisar Dattawa ta yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Kwaskwarima kamar yadda Shugaban Muhammadu Buhari ya nemi ta yi, kafin ya sa mata hannu
Gyare-gyaren Da Majalisar Dattawa Ta Yi Wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe:
Majalisar ta fara yin gyaran gaggawa kan Ƙudiri na 87, wanda ya yi magana kan irin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara daga kowace jam’iyyar siyasa.
A yanzu an amince kowace jam’iyya ta zaɓi gwanayen ta bisa tsarin ‘yar tinƙe, ƙato-bayan-ƙato ko zaɓen game-gari.
Da farko dai Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya amince a yi zaɓen kai-tsaye, ba na wakilan jam’iyya ba, wato ‘delegates’.
Wannan tsari ne ake kai a ƙasar nan, wanda kuma ƙoƙarin kawar da shi a zaɓen 2023 bai yi nasara ba, biyo bayan fatali da tsarin zaɓen kai-tsaye da Buhari ya yi bisa dalilin cewa zai ci maƙudan kuɗaɗe wajen gudanarwa.
An amince da Ƙudiri na 84, wanda ya bada damar ko jam’iyya ta yi zaɓen kai-tsaye ko kuma tsarin wakilan jam’iyya, wato ‘delegets’.
An kuma amince da Ƙudiri na 84(2), wanda ya bada damar cewa jam’iyya za shirya zaɓen fidda gwani ta hanyar wakilai, ko kumà a cimma yarjejeniyar tsayar da wani ba tare da an yi zaɓe ba.
A zaɓen fidda-gwamnin ɗan takarar shugaban ƙasa, an gindaya cewa tilas sai an yi Taron Gangamin Jam’iyya a kowace jiha 36 da Abuja FCT, domin wakilan jam’iyya daga mazaɓu su yi zaɓen ‘yan takara.
Haka nan kuma ƙudirin ya ce za a shirya babban zaɓe na ƙasa, inda za a jaddada ɗan takarar da ya fi sauran ‘yan takara yawan ƙuri’u.
Premium Times Hausa ta buga labarin cewa, Sanata Ahmad Lawal ya ce “za mu yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Kwaskwarima, mu sake aika wa Buhari ya sa hannu.’
A labarin, Shugaban Kakakin Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya bayyana ce Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya kowace za ta yi zaman yi wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe Kwaskwarima a ranar Laraba, domin a cire wuraren da ake tankiya a kai, sannan su sake aika wa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu.
Lawan ya yi wannan ƙarin haske ne a ranar Talata da dare, yayin da ya ke ganawa da manema labarai, bayan ganawar da ya yi a keɓance tare da Shugaba Muhammadu Buhari.
Lawan ya ce za su yi haka ne domin a samu damar sa wa sauran ƙudirorin dokar hannu su zama doka, yadda za a gyara tsarin zaɓe a 2023.
Shugaban Muhammadu Buhari dai ya ƙi sa wa ƙudirin hannu saboda dalilan da ya kawo.
Bayan an yi ta ce-ce-ku-ce ne kuma sai Buhari ya ce zai iya sa wa ƙudirorin hannu su zama doka, amma idan an cire wuraren da ake tankiya a ciki.
Lawan ya ce, “Idan Allah ya yarda a ranar Laraba, 18 Ga Janairu Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa kowace za ta yi zaman gyaran ƙudirorin, ta yadda za a gaggauta aika wa Shugaban Ƙasa ya sa hannu.
“Aiki ne da za mu iya kammalawa a rana ɗaya mu aika masa. Amma idan aikin ya wuce yau, to mu da aika masa sai farkon mako mai zuwa.
“Na san dai tabbas za su yi gyaran ne yadda za a ƙyale kowace jam’iyya ta bi tsarin da ta ke son bi wajen zaɓen fidda gwani, wanda ke ɗaya daga cikin wuraren da Buhari bai amince a yi zaɓen kai-tsaye, ‘yar-tinƙe ko ƙato-bayan-ƙato ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Gwamnonin PDP sun nemi Majalisar Najeriya ta yi wa Buhari ‘Sawun-giwa-take-na-raƙumi’
Gwamnonin da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun yi kakkausan kira ga Majalisar Dattawa da ta Tarayya cewa su sa ƙafar da dokar Najeriya ta ba su izni, su take hukuncin da Shugaba Buhari ya ɗauka na ƙin sa wa Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe hannu, su sa masa hannun kawai.
Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ce kuma suka bayyana wa manema labarai, a cikin takardar bayanan bayan taron da su ka karanta wa ‘yan jarida, bayan kammala taron su ranar Litinin a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.
Sun ce babu wani zaɓin da ya rage wa ‘yan majalisa dattawan su da wakilan su, sai kawai su danƙara wa dokar hannu, su yi wa matakin da Buhari ya ɗauka abin nan da ake kira ‘sawun-giwa-take-na-raƙumi.’
A ranar Talata ɗin nan ce Majalisa ke komawa aiki, bayan hutun Kirsimeti da na Sabuwar Shekara da suka tafi. Kuma an haƙƙaƙe cewa batun ƙudirin ne zai tada ƙura sosai idan majalisun biyu sun zauna.
Su kuma gwamnonin PDP sun yi kira ga Majalisa “ta yi watsi da dalilan Buhari na ƙin sa wa dokar hannu, su sai su saka mata.”
Sun ce hakan zai zama “gargaɗi ga Buhari cewa kada ya sake irin wannan hukuncin-gabagaɗi. Domin bai kamata shugaban ƙasa ya sa ƙafa ya murtsuke matakan gyaran tsarin dimokraɗiyya ba.”
Gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto, wanda kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP ya karanta wa manema labarai takarar bayan taron, wadda ke ƙunshe da wannan buƙata ta su.
Sannan kuma gwamnonin PDP sun ɗora laifin ƙara taɓarɓarewar tsaro a kan Gwamnatin Tarayya, domin ta ƙi amincewa kowace jiha ta kafa ‘yan sandan kan ta, domin shawo kan ta’addanci da hare-haren ‘yan bindiga.
“Taron na mu ya nuna matuƙar damuwa ganin yadda Shuagan Ƙasa ke maida hannun agogo baya, kan harkar tsaro da kuma gyaran dokar zaɓe.”
Sun ce kafa ‘yan sandan jiha abu ne mai muhimmanci ga daƙile ‘yan bindiga, haka gyaran dokar zaɓe na da muhimmanci ga dimokraɗiyya.
Sai dai Buhari ya ce idan aka kafa ‘yan sandan jiha, za su zama ‘yan amshin Shatan gwamnoni.
Gwamnoni 10 ne daga cikin 13 na PDP su ka halarci taron, wanda Gwamna Nysom Wike na Ribas ya zama mai masaukin baƙi.
Maida Hannun Agogo Baya: Yadda Buhari Ya Aika Wa Majalisar Dattawa Wasiƙar Fatali Da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe:
Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya wasiƙar sanar da su cewa bai yarda da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2021 ba, don haka ba zai sa wa dokar hannu ba.
Fatali da ƙudirin na ciki wasiƙar da Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya a ranar Talata ɗin nan, kuma majalisun biyu duk su ka karanta wasiƙun na shi a zaman ranar Talata ɗin nan.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ne su ka karanta wasikar ga mambobin majalisar baki ɗaya.
Dama dai tun a ranar Juma’a ne 19 Ga Nuwamba, Majalisar Dattawa ta aika wa Buhari da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe ɗin.
A cikin doguwar wasiƙar da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya karanta, Buhari ya bayyana dalilan sa na ƙin sa wa ƙudirin hannu don ya zama doka.
Buhari ya ce ya karɓi shawarwari daga Ma’aikatun Tarayya, Ɓangarorin Hukumomi da Cibiyoyin Gwamnati.
Daga nan ya bayyana batun kuɗaɗe da batutuwan shari’u a matsayin dalilan sa na ƙin sa wa ƙudirin hannu.
“Idan aka yi wa dokokin zaɓen kwaskwarima, to karya karsashin dimokraɗiyya kenan. Wannan kuwa shi ne ‘yancin da kowace jam’iyya mutum ya ga dama ya shiga ya zama mamba.
“Sai dai kuma a shekara mai zuwa majalisa za ta iya zaɓen hanya mafita idan an dawo daga hutun ƙarshen shekara.
Makonni biyu da su ka gabata ne wannan jarida ta buga labarin cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta aika wa Fadar Shugaban Kasa wasiƙar amincewa da Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta aika wa Fadar Shugaban Ƙasa wasiƙar da batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe ya ƙunsa.
Sai dai kuma INEC ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya tuntuɓi jam’iyyun siyasa da ɓangarorin jami’an tsaro, dangane da kudirin da aka shigar cewa zaɓen ‘yar-tinƙi jam’iyyu za su riƙa yi a wurin zaɓen fidda-gwanin ‘yan takara.
A ranar 29 Ga Nuwamba ce Majalisar Dattawa ta aika wa Shugaba Buhari Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe, wanda shi kuma a bisa doka, ya na da kwanaki 30 kacal da zai ɗauka ya sa wa ƙudirin hannu, domin ya tabbata doka kenan.
Shi dai wannan sabon ƙudiri, matsawar Shugaba Buhari ya sa masa hannu, to ya shafe Dokar Zaɓen ta 2010 kenan, wadda ita ce aka yi wa kwaskwarima.
A cikin kwaskwarimar dai an nemi a riƙa yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen fitar da ‘yan takara.
Sai kuma batun suka sakamakon zaɓe ta yanar gizo da sauran na’urori da kafafen sadarwa na zamani.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari ne ya rubuta wa INEC wasiƙa, inda ya nemi hukumar ta rubuto shawarwari ga Buhari, kan batutuwan da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe su ka ƙunsa.
Gambari ya shaida wa INEC cewa kada shawarwarin su wuce ranar 3 Ga Disamba.
Batun a koma yin zaɓen ‘yar-tinƙi wajen zaɓuka na fidda-gwanin takarar jam’iyyu ya haifar da ka-ce-na-ce a cikin jam’iyyar APC mai mulki. Yayin da ‘yan majalisa waɗanda mafi rinjaye ‘yan APC ne, su da ɓangaren Bila Tinubu ke goyon bayan ‘yar-tinƙe, su kuma yawancin gwamnoni sun fi so a bar tsarin yadda ya ke, wato wakilai tun daga mazaɓu har zuwa sama su riƙa yin zaɓen fidda-gwani.