Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi ta bayyana cewa Najeriya na bukatan na’urorin kula da masu fama da cutar daji 300 domin dakile yaduwar cutar a kasar.
Shugaban kungiyar NCS Adamu Alhassan ya fadi haka a taron da ya yi da manema labarai a Abuja domin tunawa da ranar cutar daji ta shekarar 2022.
Alhassan ya ce adadin yawan na’urorin kula da masu fama da cutar da ake da su a Najeriya guda 10 ne kacal.
Ya ce a dalilin haka ya sa masu fama da cutar ke fama da matsaloli da dama.
Alhassan ya ce matsalolin ya karu saboda rashin saka cutar a cikin tsarin inshorar da gwamnati ta ki yi.
Yaduwar cutar daji a Najeriya.
Gidauniyar ‘Union for International Cancer Control (UICC)’ ce ta kebe ranar 4 ga Fabrairu na kowace shekara domin wayar da kan mutane game da cutar daji.
Daji na daga daga cikin cututtukan dake kisan mutane a duniya.
Cutar daji kan kama mutum ne idan wani bangare na jikinsa ya fara girma fiye da yadda ya kamata.
Cutar kan kama babba ko yaro a kowani gaban jikin mutum sannan idan ba an gano cutar da wuri ba kuma an fara magani da wuri cutar ka iya ajalin mutum.
Sakakamon WHO ya nuna cewa mutane 116,000 ne suka kamu da cutar sannan cutar ta yi ajalin mutum 41,000 a Najeriya a shekaran 2018.
Tsadn farashin magani da rashin samun kula na daga cikin matsalolin da masu fama da daji ke fama da su a Najeriya.
Idan har aka ci gaba a haka za a samu mutum 1,055,172 da za su rika kamuwa da cutar sannan cutar za ta rika kisan mutum 2,123,245 daga nan zuwa shekaran 2040.
Sakamakon binciken da hukumar gudanar da bincike kan cutar daji ta ƙasa da ƙasa ta gudanar ya nuna cewa mutum daya cikin maza biyar da mace daya cikin mata shida za su iya kamuwa da cutar.
Binciken ya kuma nuna cewa cutar za ta iya kashe namiji daya cikin maza 8 da mace daya cikin mata 11 a duniya.
Na’urorin kula da masu fama da cutar daji
Rashin samun kula da tsadan farashin magunguna na daga cikin matsalolin da masu fama da daji ke fama da su a kasar nan.
Kwararrun likitoci sun ce ‘Radiotherapy’ na cikin kulan da ake yi wa mai dauke da cutar.
Sannan bisa ga tsari bai kamata mai fama da wannan cuta da ya fara samun kula na Radiotherapy ya tsaya a hanya ba domin yin hakan ne ke dawo da hannu ago baya wajen kawar da cutar a jikin mutum.
A Najeriya adadin yawan na’urorin kula da masu fama da cutar da ake da su guda 10 ne inda 9 na asibitocin gwamnati sannan biyu a asibitocin dake zaman kansu.
Samun kula na cutar daji
Kodinatan AHBN Aminu Magashi ya koka da yadda masu fama da cutar ke fama da tsadar farashin magunguna da rashin samun kula a Najeriya.
Magashi ya ce kamata ya yi mai fama da cutar ya samu kula ta gari.
Ya yi kira ga gwamnati da ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya domin taro hanyoyin da mutane za su kiyaye domin guje wa kamuwa da cutar.